in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da firaministan Kasar Sin zai yi za ta taimaka wajen zurfafa huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka
2014-05-08 16:09:47 cri

Ziyarar da firaministan kasar Sin Li Keqiang zai gudanar a nahiyar Afirka tun daga ran 4 zuwa ran 11 ga watan Mayu a shekarar da muke ciki, wata muhimmiyar dama ce ga kasar Sin da takwarorinta na nahiyar Afirka wajen dada zurfafa dangantakar abokantaka dake tsakaninsu tsawon lokaci.

Tarihin wannan dangantaka dai na komawa ne ga shekaru 50 da suka gabata, lokacin da tsohon firaministan kasar Sin Zhou Enlai ya ziyarci nahiyar. Ziyarar da ake kallo a matsayin ginshiki na dorewar alakar sassan biyu.

A ranar 8 ga watan Maris da ya gabata ne dai ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tabbatar da shirin da ake yi na ziyarar ta Mr. Li a Afirka. Wadda ya ce ta zo daidai lokacin da dangantaka tsakanin sassan biyu ke shiga wani sabon matsayi na bunkasa.

Mr. Wang wanda ya bayyana wannan muhimmiyar ziyara da Li Keqiang zai kai Afirka a karon farko, tun bayan kasancewarsa firaministan kasar Sin ya lasafta dalilan gudanar da ita tare da irin tasirin da take da shi ga bangarorin biyu.

Da farko Wang ya ce kasar Sin da kasashen Afirka abokai ne, kuma 'yan uwa dake neman ci gaba tare. Kuma kasar Sin na tallafawa kasashen Afirka ta dukkanin hanyoyin bunkasuwa ba tare da sanya wani sharadi ba. Har wa yau kawo yanzu kasar Sin ba ta taba yiwa kasashen Afirka alkawarin da ba ta cika ba. Cikin irin wannan alkawura a cewar Mr. Wang kasar Sin ta gudanar da manyan ayyuka sama da 1,000 a sassan nahiyar ta Afirka daban daban.

Bugu da kari tarihi ba zai taba mantawa da irin gudummawar da Afirka ta baiwa kasar Sin wajen dawo mata da kujerar din din din ta MDD ba. Yayin da ita kuma Sin ta tallafawa kasashen nahiyar da dama wajen samun 'yancin kansu daga Turawan mulkin mallaka.

A baya bayan nan kuwa, Mr. Wang ya ce ziyarar da ya kai nahiyar ta Afirka cikin watan Janairu, ta ba shi damar ganawa da jami'an gwamnatoci da dama, wadanda suka tabbatar masa da cewa, ci gaban da nahiyar ke samu yanzu haka, na da alaka ta kai tsaye da hadin gwiwar da suke yi da kasar Sin.  (Saminu, Sanusi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China