140407-MH370Sanusi
|
Kawo yanzu dai kasashen duniya da dama na ci gaba da tallafawa aikin neman jirgin fasinjan nan na kasar Maleshiya, wanda ya bace fiye da wata guda a kan hanyarsa ta zuwa birnin Beijing na kasar Sin daga kasar Malesiya.
Shi dai wannan jirgin sama mai lamba MH 370, ya bace ne tun ranar 8 ga watan Maris din da ya gabata, dauke da mutane 239 da suka hada da Sinawa 154.
Rahotannin da masana suka bayar sun nuna cewa, an rufe na'urar sadarwar jirgin da gangan, jim kadan da barinsa sararin saman kasar ta Malesiya. Kuma wasu sakwannin da tauraron dan Adam suka danko sun nuna cewa jirgin, ya ci gaba da tafiya kusan sa'o'i 5 bayan hakan, lamarin da ya sanya kowa damuwa da shiga halin rashin tabbas kan makomar fisinjojin dake cikin wannan jirgi.
A kuma ran 24 ga watan Maris da ya gabata, firaministan Maleshiya Mohd Najib Razak ya tabbatar cewa wannan jirgi ya fada wani wuri a kudancin tekun Indiya, kuma babu wani mutum guda da ya rayu daga cikinsa. Bayan wannan sanarwa firaministan Malaysian Mohammad Najib Razak, ya ci gaba da gudanar da taron manema labaru a kai a kai domin bayyanawa duniya halin da ake ciki.
Har wa ranar Litinin 7 ga watan Afrilu, babban jami'in cibiyar kasar Australiya mai kula da ayyukan neman jirgin saman Angus Houston, ya ce wani jirgin ruwan sojan Australiya ya jiyo amon wani abu har sau biyu daga karkashin teku, wanda ya dace da amon na'urar nadar bayanan jirgin sama, kana wurin da ya jiyo amon yana dab da inda wani jirgin ruwan kasar Sin ya jiyo amon wani abu a ranar 5 ga wata. Matakin da masu aikin ke ganin muhimmin ci gaba ne a aikin laluben jirgin da ake yi.