in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin ranar Littattafai da hakkin mallakarsu ta Duniya
2014-04-24 18:04:36 cri


Ranar 23 ga watan Afrilun kowace shekara, rana ce da hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ke gudanar da bikin ranar Littattafai da hakkin mallakarsu ta Duniya.

An dai ayyana wannan rana ne a karon farko, yayin babban taron hukumar ta UNESCO na 1995, da ya gudana a birnin Faris. Bayanai sun kuma shaida cewa, wannan rana ta dace da ranar da aka haifi da yawa daga mashahuran marubuta da suka rayu a wannan duniya, a hannu guda ta kuma dace da ranar rasuwar wasu daga cikin su.

Babban burin da ake fatan cimmawa kuwa, bai wuce karfafa gwiwar marubuta ba wajen ci gaba da ba da gudummawarsu ga al'ummar duniya, tare da tabbatar da al'umma sun dada rungumar karatu ta hanyar litattafai, musamman kasancewar littattafan wata taskar adana ilimi, dake saukaka yaki da fatara, kuma tubulin ginin zaman lafiya mai dorewa.

Kazalika ana amfani da wannan rana ta Littattafai da hakkin mallakarsu ta Duniya, wajen jinjinawa marubuta, game da gudummawar da suke baiwa ci gaban rayuwar bil'adama.

A bana, birnin Fatakwal dake jihar Rivers a kudancin tarayyar Najeriya hukumar UNESCO ta zaba, domin ya kasancewa cibiyar litattafai ta duniya tsahon shekara guda. Ana kuma fatan hakan zai taimaka matuka, wajen raya harkar rubuce-rubuce, da karatu tsakankanin al'ummar Najeriya da ma duniya baki daya.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran gani a birnin na Fatakwal a tsawon shekarar shi ne, tarukan wasu marubuta daga fadin nahiyar Afrika. Inda marubutan za su tattauna kan batutuwa da dama, da suka shafi adabi da talifi.

Ko da yake dai batun satar fasahar marubuta, da zuwan kafofin sadarwa na zamani, ciki hadda wayoyin tarho na tafi da gidanka, da shafukan yanar gizo, da littattafai da ake iya karantawa ta na'ura mai kwakwalwa, na rage karsashin karatu tsakankanin al'umma, a hannu guda manazarta da daman a ganin littattafai za su ci gaba da rike matsayin su na koli, wajen yada ilimi da wayar da kan bil'adama.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China