in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan tsare-tsaren da kasar Sin ke aiwatarwa a fannin raya tattalin arziki na jawo hankali sosai a yayin taron shekara-shekara na IMF
2014-04-14 15:07:39 cri

A ranar 13 ga watan nan ne Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya rufe taron shekara-shekara na lokacin bazara, taron da ya gudana a birnin Washington a kasar Amurka. Shin ko wane irin muhimman batutuwa aka tattauna yayin taron na wannan karo? Mene ne kuma abubuwan da suka shafi kasar Sin wadanda suka jawo hankalin mutane?

Taron na ranar Lahadi 13 ga watan nan, wanda asusun IMF ke gudanarwa a kowace shekara a lokacin bazara, wanda aka washe yini uku ana gudanarwa, a wannan karo ya samu halartar wakilai, da jami'an gwamnati daga kasashe fiye da 100, wadanda kuma suka tattauna batutuwa daban daban da suka shafi tattalin arzikin duniya, da kasuwar hada-hadar kudi, da batun gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, da harkokin siyasa a shiyya-shiyya, da kwaskwarima kan rabon tallafi ko ayyukan IMF da dai sauransu.

Cikin wani rahoto da asusun IMF ya gabatar kafin budewar taron mai suna "hangen nesa kan tattalin arzikin duniya", an bayyana rage hasashen da aka yi a karuwar tattalin arzikin duniya da kaso 3.6 cikin dari. Haka kuma, a yayin taron manema labaru da aka yi a ranar 13 ga wata, Zhu Min, mataimakin shugaban IMF ya bayyana cewa, a lokacin taron, da farko an mai da hankali kan yadda za a raya tattalin arzikin duniya. Mista Zhu ya ce,"Kusan dai kashi 3.6 cikin dari yana da kyau, amma bai gamsar da mu sosai ba. A bana za mu shiga lokacin wucin gadi, za mu gudanar da ayyukan gyare-gyare. Za mu kuma yi amfani da adadin, domin kara karfin yin gyare-gyare da kyautata wasu abubuwa, a kokarin aza harshashi mai kyau, na samar da ci gaba mai dorewa a bana da kuma badi."

Mista Zhu ya kara da cewa, ko da yake a bana Amurka da kungiyar Tarayyar Turai, da sauran rukunonin tattalin arziki masu sukuni za su taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, duk da hakan suna dogara da manufofinsu ne na wucin gadi na tsuke bakin aljihu, da suke gudanarwa a halin yanzu. Sakamakon gazawa wajen ci gaba da aiwatar da irin wadannan manufofi a kasashe masu sukuni, rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki, da kasashen da ke samun kudin shiga kalilan, ya sa kasashen duniya suka fahimci wajibcin yin gyare-gyare kan tsare-tsaren tattalin arziki.

Mista Zhu ya yi nuni da cewa, a shekaru 5 da suka wuce, manufofin kasashe masu sukuni, na sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arziki sun kara azama, ga rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki wajen zuba jari a gida da kuma bunkasuwarsu, yanzu sakamakon daina aiwatar da wadannan manufofi a mataki mataki, ya sa yanayin da rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki ke ciki ya sauya, don haka ya zama tilas su tsaya da kafarsu wajen bunkasa tattalin arziki. Har wa yau ko da yake yanzu haka kyakkyawan ci gaban tattalin arzikin rukunonin tattalin arzikin masu sukuni, yana taimakawa rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki sosai wajen sayar da kayayyakinsu a ketare, amma kasashe masu sukuni da dama, suna kara dogaro da sayar da kayayyaki zuwa ketare domin raya tattalin arzikinsu, lamarin da zai kara zafin takara a tsakanin rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a fannin sayar da kaya a ketare. Mista Zhu ya ce, "Ana sa ran cewa, yawan karuwar tattalin arzikin rukunonin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki zai kai kashi 4.9 cikin dari a bana, hakan na da kyau ainun. Amma dole ne su lura da sauye-sauyen da aka samu a yanayin da suke ciki, kana su kyautata yin gyare-gyare kan gazawar su a gida. Har wa yau kuma wajibi ne su lalubo hanyar bunkasa tattalin arzikinsu da kansu, ta haka za su iya samun bunkasuwa mai dorewa."

Bugu da kari, mista Zhu ya bayyana cewa, a yayin taron, kasar Sin, wadda ke matsayi na biyu na rukunin tattalin arziki mafi girma a duniya, ta jawo hankalin jama'a sosai. Zhu ya ce,"Ministocin kudi da shugabannin babban bankunan kasa da kasa, sun yaba wa kwanciyar hankali da kasar Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki. Suna ganin cewa, kasar Sin na tabbatar da raya tattalin arzikinta da kashi 7 zuwa 7.5 cikin dari, hakan na da kyau sosai, domin matsayine da ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A lokacin taron, kasashe da dama, musamman ma kasashen Afirka da na Latin Amurka, wadanda suke da dankon hulda a tsakaninsu da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, sun mai da hankali kan manyan tsare-tsaren da kasar Sin ke aiwatarwa wajen raya tattalin arziki, a maimakon harkokin tattalin arzikin duniya."

Duk da haka, mista Zhu ya ce, mahalarta taron sun nuna damuwarsu kan boyayyiyar barazanar da kasar Sin ke fuskanta a harkokin tattalin arziki. Mista Zhu ya ce, "Kwanan baya, shugabar asusunmu ta gana da firministan kasar Sin, yayin da ta halarci wani taro a kasar ta Sin, inda kuma ta gana da wasu manyan jami'an kasar. Bayan ganawar, ta nuna karfin gwiwa kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba tare da matsala ba, musamman a fagen yin gyare-gyare kan tsare-tsaren tattalin arzikin kasar, da kawar da matsaloli a harkokin kudi, wanda hakan ya karfafa zuciyar mahalarta taron."

A sa'i daya kuma, Zhu Min ya nuna cewa, yayin da kasar Sin ke kokarin raya tattalin arzikinta cikin daidaito, za ta rage zuba jari, lamarin da zai kawo illa ga wasu kasashen da suka sayar wa kasar ta Sin kayayyaki.

Ana bukatar kasashen duniya su kyautata manufofinsu bisa ga matakan da kasar Sin za ta dauka, matakin da yanzu haka kasashen duniya suka fahimta. Musamman duba da cewa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin daidaito za ta taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China