140411-balain-fari-na-kara-bazuwa-a-arewacin-Kenya-Danladi
|
Daga watan Maris har zuwa yanzu, bala'in fari na kara bazuwa a yankin Turkana da ke arewacin kasar Kenya. Hukumar da ke gudanar da aikin ceto a wurin ta sanar da cewa, jama'a fiye da dubu 450 suna bukatar taimakon abinci da ruwa cikin gaggawa. Shin ko wane irin tasiri bala'in farin yake haifarwa mazaunan wurin? Kuma ko me yasa ba a iya magance matsalar ruwa ba, bayan da aka sanar da gano ruwa mai yawa a karkashin kasa?
Daga watan Maris kawo yanzu, damina ta yi jinkiri a yankin Turkana da ke arewacin kasar Kenya, sakamakon haka, mazaunan wurin suna cikin wani mawuyacin hali.
'A ko wace rana, ni da yara na mu kan ci 'ya 'yan itatuwa da ke fitowa da kansu. Sakamakon wannan bala'in fari, awakina guda 10 sun riga sun mutu, kuma yara na biyu sun rasu'
Ta ci gaba da cewa,
'A wasu lokuta, muna kwana da yunwa. Dukkan dabbobin da nake kiwo na kore su wurare masu nisa, ko da yake wurare ma na fama da karancin ruwa can, amma da akwai 'yan ciyayi. Dabbobi da yawa sun mutu sakamakon bala'in fari, kana iya ganin gawawakinsu a wajen dakina.'
Da akwai wani kauye mai suna Narsete a yankin Turkana, da aka tabo magana kan bala'in fari, mazaunan wurin sun nuna bakin cikin su.
Wakilinmu ya kai ziyara a wannan kauye, ya ga babu wasu motoci da ke wucewa, babu mutane da ke hada-hada, sai mazaunan wurin 'yan kadan a kusa da gidajen su, da kuma rakuma da awaki 'yan kadan dake kewayawa a cikin kauye.
Shugaban wata kungiyar mai zaman kanta mai suna 'Practical Action Organization', da ke bayar da taimakon abinci a wuin, Willie Tuimising, ya gaya wa wakilinmu cewa, a yankin Turkana, akwai kauyuka masu yawan gaske kamar Narsete da ke fama da bala'in fari.
'A halin yanzu, jama'ar da yawansu ya kai dubu 450 suna fuskantar babbar illa daga bala'in fari. Sakamakon jinkirin damina, adadin zai iya kara karuwa. Ban da wannan kuma, makiyaya kusan dubu 35 sun riga sun wuce kan iyaka zuwa kasar Uganda.'
Bisa labarin da muka samu, an ce gwamnatin kasar Kenya ta bayar da wata kididdiga a watan Satumbar bara, dake nuna cewa binciken da aka yi ya nuna akwai wasu sassa na karkashin kasa 5 da ke kwari guda 5 da ke da ruwa, haka kuma sassa 2 daga cikinsu gwamnati ta gano ruwan da ya kai cubic mita a kalla biliyan 250, wanda Kenya ba za ta iya kare amfani da shi a cikin shekaru 70 masu zuwa ba. Game da haka, wasu sun yi hasashen cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa, ba za a samu 'yan Turkana da zasu rasu sakamakon yunwa da rashin ruwa ba.
Amma ganin yadda ake fama da karancin ruwa a halin yanzu, Shehun malami da ke nazarin yanayin karkashin kasa a Jami'ar Nairobi Mista Justus Barongo, ya gaya wa wakilinmu cewa, bala'in fari da ake fuskanta a halin yanzu ya zama wani abin kunya, duba da cewa an gano ruwa a karkashin kasa. A ganin sa, ba a gudanar da wani aiki na tono ruwan daga karkashin kasa ba, balle amfani da shi bisa manyan bukatun al'umma ba. Ya ce wasu matsaloli masu alaka da fasahohi sun hana aikin samun ruwan a karkashin kasa.
Amma wani babban jami'in kula da harkokin amfani da ruwa, na ma'aikatar albarkatun ruwa ta kasar ta Kenya John Nyaoro, yayi imanin cewa za a kai ga samun amfani da ruwan da ke karkashin kasar. A cewarsa, gwamnati za ta daidaita matsalolin fasahohi bisa matakai daban daban, kuma tuni ma aka fara samun nasarori a wasu fannonin da suka shafi hakan. (Danladi)