140411-A-bikin-Qingming-Sinawa-su-kan-yi-yawon-shakatawa-musamman-kalon-furrani-Danladi
|
Ranar 5 ga watan Afrulu ne, ya zama bikin Qingming na kasar Sin. A lokacin bikin Qingming, Sinawa ba su aiki ba, gwamnati ta ba su kwanaki uku mu huta mu je wurare daban daban don yawon shakatawa. Sabo da lokacin bikin Qingming yana cikin lokacin bazara wato lokacin da itatuwa sun fara girma, furanni sun fara budewa. Sabo da haka ne a kan dasa itatuwa, a je wurare daban daban don kallon budewar furanni.
Kallon budewar furanni ya riga ya zama wani abin gargajiya da Sinawa suka yi a ko wace shekara. A halin yanzu wurare daban daban na kasar Sin sun shirya bukukuwa da yawa wajen kallon furanni, ga misalai, da waki bikin nuna budewar furannin Peach da ke jihar Tibet , da bikin nuna al'adun furannin Peony a birnin Luoyang da ke lardin Henan na kasar Sin.
Ban da Tibet da Luoyang kuma, kamfanonin kula da harkokin yawon shakatawa na kasar Sin sun shirya wasu layi da yawa don kallon furanni ciki har da dutsen Huangshan da ke lardin Anhui, da garin Wuyuan da ke lardin Jiangxi, da yankin Taihu da ke lardin Jiangsu da garin Yangzhou da ke lardin Jiangsu da dai sauransu. Duk dai an hada su, don jama'a suke iya kallon dukkan furanninsu a lokacin hutu na Qingming. (Danladi)