in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hajia Amina Jummai Gimba dake taimaka wa masu fama da lalurar Autism
2014-04-09 18:26:33 cri

A shekarar bara, wakiliyar aikinmu Fatimah Jibril ta samu damar hira da Hajiya Amina Jummai Gimba, wata baiwar Allah kuma Uwa da Allah ya jarabce daya daga cikin 'ya'yan ta da wata lalura ta dushewar tunani da ake kira da turanci AUTISM. Amma matsala bata sa ta karaya ba a'a sai ma ta samu kwarin gwiwar kafa wata cibiyar musamman domin taimaka ma sauran yara masu fama da wannan lalura.

Ganin ranar 2 ga watan Afrlilu, ita ce ta zama ranar da MDD ta kebe domin tunawa da masu fama da wannan lalurar ta Autism, saboda haka ne, wannan shiri ya waiwayi hirar da Fatimah ta yi tare da wannan bakuwar tamu, da zata gabatar da kanta, kafin ta mana karin haske kan rayuwarta da ma larurar data shafe danta da kuma ayyukan da take yi don taimakon masu irin wannan lalura.

To a makon da ya wuce mu sake tuntubar Hajiya Amina Jummai Gimba ta yi mana bayani game da shirin da cibiyarta ta yi musamn domin fadakar da al'umma game da wannan lalura ta AUTISM da kuma wani taron bita da Hukumar kula da jami'o'in na kasa wato NUC ta shirya a Abuja wanda ta kasance cikin mahalarta taron.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China