140404-an-bikin-Qingming-na-kasar-Sin-jamaa-su-kan-nuna-tunawarsu-ga-iyalan-da-suka-rasu-Danladi
|
A ranar 5 ga watan Afrilu, bikin Qingming ne na gargajiya na kasar Sin. Bikin Qingming daya daga cikin bukukuwa 24 na yanayi bisa ga kalandar hasken wata ta kasar Sin.
Bukukuwan yanayi da muhalli na kasar Sin suna da tarihin na tsawon shekaru fiye da dubu biyu, sun kasance bukukuwan al'adu da jama'ar kasar Sin suka samu bayan nazari da kuma takaita abubuwa kan yanayin sararin samaniya cikin 'yanci kuma cikin dogon lokaci. Suna iya bayyana sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ruwan sama da sauran sauye-sauyen da aka samu bisa yanayin sararin samaniya da kuma ba da jagoranci ga ayyukan noma, da ba da tasiri sosai ga abinci da sutura da tafiye-tafiye na duban iyalai. A takaice dai, an kasa shekara daya cikin matakan lokaci 24 bisa yanayin sararin samaniya, a kowane matakin, alamar yanayin sararin samaniya ta zauna cikin zaman karko, kuma kowane lokaci yana da na shi suna. Bikin Qingming ya kan zo a ranar 4 ko biyar ko shida ga watan Afril. Bikin Qingming na shekarar da muke ciki zai zo ne a ranar 5 ga watan Afril.
Tunawa da mutanen da suka riga-mu gidan gaskiya a gaban kabaransu aiki ne mai muhimmanci da ake yi a ranar bikin Qingming. Kabilar Han da sauran kananan kabilu su ma suna da irin wannan al'adar koda yake a wasu kauyukan kasar Sin, a ranar bikin Qingming, mutane suna zuwa wajen makabatun da aka binne kakani-kakaninsu da na danginsu tare da giya da abinci da 'ya'yan itatuwa da kyandir da turare da sauransu, sa'anan su kunna kyandir da turare, su ajiye abinci a gaban kaburan 'yan uwansu, su kara sanya kasa a kan kabarin tare da yanke wasu rassan bishiyoyi don dasa su a kan kaburan, sannan su rika sujada tare da watsa giya da abinci a gaban kaburan . A ranar bikin Qingming , ana ruwan sama a wurare da yawa a kasar Sin, wannan ya kara sanya mutane cikin tunanin danginsu da suka riga mu gidan gaskiya, wani mashahurin mawaki na karni na 9 mai suna Du Mu ya taba rubuta halin nan na musamman da ake ciki da cewa, ana ta ruwan sama , mutanen da ke tafiya a kan hanya suna cikin bakin ciki sosai tamkar yadda za su mutu bisa sakamakon tunawa da danginsu da suka riga mu gidan gaskiya. (Danladi)