in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi a kan manufar kasar Sin game da tsaron nukiliya
2014-03-25 17:32:30 cri

A gun taron kolin tsaron nukiliya da aka bude a ranar 24 ga wata a birnin Hague na kasar Holland, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi inda ya bayyana manufar kasar Sin a kan tsaron nukiliyar. A wannan rana kuma, a tattaunawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, babban sakataren kungiyar kula da kayyade makamai da kwance damara ta kasar Sin, Mr.Chen Kai ya bayyana cewa, manufar kasar Sin kan tsaron nukiliya ta shaida yadda kasar ke sauke nauyin da ke bisa wuyanta a matsayinta na wata babbar kasa, wadda kuma ta kasance mai ba da muhimmiyar gudummawar kyautata tsaron nukiliya a duniya baki daya.

A gun taron, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana manufar kasar Sin a kan tsaron nukiliya, wato na farko ya kamata a sanya muhimmanci na bai daya game da raya makamashin nukiliya da ma tabbatar da tsaronta, na biyu a sanya muhimmanci iri daya a kan hakkin kasa da kasa na raya makamashin nukiliya da na nauyin dake kansu wajen kiyaye tsaronsa, na uku a sanya muhimmanci iri daya bisa karfin daidaikun kasashe da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, na hudu a sanya muhimmanci iri daya a kan daidaita matsalolin da ake fuskanta tare da ainihin abubuwan da ke haddasa matsalolin, manufar da a ganin Chen Kai, babban sakataren kungiyar kayyade makaman soja da kwance damara ta kasar Sin, ke kunshe da dukkanin muhimman abubuwan da ya kamata a bi wajen sanya shirin kiyaye tsaron nukiliya kan hanyar bunkasa yadda ya kamata kuma bisa turba mai dorewa.

A game da sanya muhimmanci bai daya kan bunkasa makamashin nukiliya da tabbatar da tsaronsa, Mr.Chen Kai ya bayyana cewa, raya makamashin nukiliya abu ne da kasashe da dama ciki har da kasar Sin ke bukata wajen raya kansu, duk da haka, tabbatar da tsaronsa babban sharadi ne da aka gindaya a kansa, sabo da makamashin nukiliya zai iya kawo babbar masifa in dai ba a iya tabbatar da tsaronsa.

Sa'an nan, a game da sanya muhimmanci bai daya a kan hakkin kasa da kasa na raya makamashin nukiliya da nauyin kiyaye tsaronsa, Mr.Chen Kai yana ganin cewa, an bayyana hakan ne a sanadin yadda kasa da kasa ke fama da bambanci ta fuskar raya makamashin nukiliya da kuma kiyaye tsaronsa. Don haka, a cewarsa, ya kamata kasa da kasa su bi dokoki da ka'idojin duniya da suka shafi kiyaye tsaron nukiliya, tare da ba su damar tabbatar da matakan da za su dauka da za su  dace da yanayinsu da kuma bukatunsu don cimma burin kyautata tsaron nukiliya.

Har wa yau, Mr.Chen Kai ya ce, tabbatar da tsaron nukiliya babban aiki kan dukannin kasashe, haka kuma aiki ne da kasashen duniya baki daya ke fuskanta tare, don haka ne shugaban kasar Sin a furucinsa ya bayyana sanya muhimmanci iri daya a kan ikon kasashe da kuma na hadin gwiwarsu. Chen Kai ya ce, tabbatar da tsaron nukiliya nauyi ne da ke kan kowace kasa, don haka, abu mafi muhimmanci shi ne kasa da kasa su tabbatar da tsaron nukiliyarsu. A sa'i daya kuma, ya zama dole kasa da kasa su hada kansu a yayin da ake yakar ta'addancin da ya shafi nukiliya da kuma hana fasa-kwaurin kayayyakin nukiliya.

Daga karshe, Mr.Chen Kai ya yi nuni da cewa, "sanya muhimmanci iri daya a kan daidaita matsalolin da ake fuskanta da kuma kawar da ainihin abubuwan da suka haifar da matsalolin" manufa ce da aka gabatar a sanadin yadda kasar Sin ta fahimci ainihin dalilan da suka haifar da matsalolin da ake fuskanta. Ya ce, yanzu haka kasa da kasa na kokarin raya karfinsu da hadin gwiwa tsakaninsu tare kuma da tsara dokoki, a wani kokari na ganin an tabbatar da tsaron nukiliya, duk da haka, an fi mai da hankali ne a kan tinkarar matsalolin da aka gano, a maimakon ainihin abubuwan da suka haddasa matsalolin.

"Domin kawar da ainihin abubuwan da suka haifar da matsalolin da ake fuskanta ko kuma a rage su, dole ne kasashe daban daban su yi kokarin tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a shiyya shiyya da kuma duniya baki daya, a sassauta fatara, kuma a tabbatar da mu'amala da fahimtar juna a tsakanin kasashe daban daban", in ji Chen Kai. Bugu da kari, ya kara da cewa, "kasar Sin na dukufa a kan samar da yanayi mai kyau a duniya, matakin da babu shakka zai taimaka ga sassauta ainihin abubuwan da ke haddasa ta'addanci." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China