in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tattauna kan hanyoyin dakile amfani da makaman nukiliya wajen aikata ta'addanci
2014-03-24 15:22:52 cri

Kafin taron koli game da tsaron nukiliya da za a shafe kwanaki biyu ana gudanarwa a birnin Hague na kasar Holland, mai masaukin taron, firaministan kasar Holland Mark Rutte ya bayyana cewa, amfani da makaman nukiliya wajen aikata ta'addanci yana daya daga cikin manyan kalubalolin dake barazana ga tsaron duniya, saboda haka a yayin taron wannan karo, za a dukufa wajen karfafa tsaron nukiliya a dukkanin fadin duniya.

Shugaba Barack Obama na kasar Amurka ne ya gabatar da bukatar shirya taron na koli game da batun tsaron nukiliya a shekarar 2009, aka kuma gudanar da shi a shekarar 2010 a birnin Washington na kasar Amurka. Daga baya kuma a shekarar 2012 aka sake gudanar da taron a karo na biyu a birnin Seoul na kasar Koriya ta kudu.

A yayin wannan taron karo na uku, an sanya batun "karfafa tsaron nukiliya, da hana amfani da makaman wajen aikata ta'addanci" a matsayin babban taken taron, da nufin ciyar da tsarin tsaron nukiliya na duniya gaba. Taron na wannan shekara kuma ya samu halartar shugabanni na kasashe 53, da jami'ai daga MDD, da kungiyar tarayyar kasashen Turai, da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, da kuma hukumar 'yan sanda ta duniya.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 23 ga wata, firaministan kasar Holland, Mark Rutte ya bayyana cewa, amfani da makaman nukiliya wajen aikata ta'addanci, wani babban kalubale ne da ake fuskanta a duniya, kuma abubuwan da za a tattauna a yayin taron kolin na kwanaki biyu sun shafi tsaron al'ummar duniya baki daya.

"'yan ta'adda ba su da damar mallakar makamashin nukiliya, hakan abun farin ciki ne. Amma idan hakan ta auku, za a fuskanci matsaloli masu tsanani kwarai. Akwai bukatar mu hana amfani da makaman nukiliya wajen aikata ta'addanci, shi ne kuma burinmu na haduwa a nan. Makamashin nukiliya na da amfani a fannoni da dama, ciki har da samar da wutar lantarki, da aikin jinya, amma idan sun fada hannun mutanen da ba su kamata ba, mai yiwuwa ne a yi amfani da su wajen kirar makaman nukiliya," a kalaman Mr. Rutte.

Har illa yau Mark Rutte ya bayyana cewa, ko da yake an samu nasarori a wasu fannoni a yayin taron koli na Washington, da na Seoul, sai dai a hannu guda akwai ayyuka da dama da za a yi, don tabbatar da amfani da makamashin nukiliya yadda ya kamata. Ya ce, a yayin taron koli na Hague, shugabanni mahalarta taron za su bayyana manufofin da kasashensu suke bi a wannan fanni, tare kuma da tattauna matakan da suka dace, don magance aikata ta'addanci ta hanyar amfani da makaman nukiliya.

"Muna kokarin neman hanyoyin da za a bi don hana 'yan ta'adda samun makamashi, da birbishin guba ta nukiliya, ciki har da rage yawan sinadaran nukiliya masu hadari a duk duniya, da daukar matakai don kiyaye sinadaran nukiliya, kana da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fannin," a ta bakin Rutte.

A dai wannan rana ta 23 ga wata dai, ita ma cibiyar watsa labarai ta tawagar kasar Sin, wadda ke halartar taron kolin ta soma aikinta. Inda shugaban cibiyar, kuma mataimakin sashen watsa labaru na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, madam Hua Chunying ta bayyana cewa, shekarar 2009 ce karon farko, da tawagar kasar Sin ta kafa cibiyar watsa labarai a yayin taron tattaunawa da aka shirya tsakanin shugabannin kungiyar G8 da na kasashe masu tasowa a kasar Italiya.

Haka zalika wannan taron koli na Hague ne karo na 28 da kasar Sin ta kafa cibiyar watsa labaru a yayin taron da shugabanninta ke halartar muhimman taruka, ko wata muhimmiyar ziyarar aiki. Madam Hua Chunying ta ce,

"Bisa bunkasuwar da kasar Sin ta samu, tana ta kara shiga harkokin duniya, hakan dai ana fatan zai sanya kasashen duniya kara fahimtar matsayin da Sin ke dauka, da sauraren muryarta cikin lokaci. A bangaren guda kuma, kamata ya yi mu yi aniyar sauke nauyin bai wa abokanmu 'yan jarida hidimar samun labaru masu amfani yadda ya kamata."

Hua Chunying ta kara da cewa, taron koli game da tsaron nukiliya na Hague ya kasance karo na farko, da sabon shugaban kasar Sin ya halarta a fannin tsaro, kuma muhimmin mataki ne da kasar Sin take dauka a wannan fanni. A yayin taron, cibiyar watsa labaru ta tawagar Sin za ta gayyaci jami'ai, da kwararru a wannan fanni domin su bayyanawa manema labaru tasirin halartar shugaba Xi Jinping na kasar Sin wannan taro. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China