in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mata a majalisun kasar Sin
2014-03-10 16:31:05 cri


Wani rahoto mai taken "mata a majalisa" da kungiyar tarayyar majalisun kasa da kasa ta fitar a ranar 4 ga wata a Geneva ya nuna cewa, a shekarar 2013, yawan mata 'yan majalisa a kasashen duniya ya karu da kashi 1.5% bisa na shekarar da ta gabata, wato ke nan, in an samu dorewar wannan ci gaba, mata za su tashi daya da maza a majalisun kasashen duniya nan da shekaru 20 masu zuwa. Rahoton ya kuma bayyana cewa, yawan mata a majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya wuce matsakaicin yawan mata a majalisun kasashen duniya.

Kungiyar ta tarayyar majalisun kasa da kasa ta fitar da wannan rahoto ne a dab da ranar da aka kebe wa matan duniya, wato ranar 8 ga watan Maris, kuma a daidai lokacin da ake gudanar da manyan taruka biyu a nan kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar, don haka, yau za mu leka rawar da mata ke takawa a majalisun kasar Sin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China