in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude taron NPC ba da jimawa ba
2014-03-04 17:34:17 cri

A gobe Laraba 5 ga wata ne za a bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC), majalisar da ta kasance hukumar koli ta kasar, inda wakilan jama'a sama da 2000 da suka zo daga sassa daban daban na kasar za su taru a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar ta Sin, don tattauna manyan harkokin da suka shafi ci gaban kasar , tare da ba da shawarwarinsu. A yau da safe, an kira taron manema labarai, inda kakakin taron, Madam Fu Ying ta amsa tambayoyin manema labarai na gida da na waje dangane da batutuwan da suke daukar hankalin bangarorin daban daban, ciki har da batun kafa dokoki da kiyaye muhalli da kasafin kudin tsaron kasa, da zurfafa matakan gyare-gyare da sauransu, inda kuma ta jaddada cewa, kasar Sin za ta ba da jagoranci ga gyare-gyaren da take yi ta hanyar kafa dokoki.

Da farko, Madam Fu Ying ta yi bayani kan ajandar taron, inda ta ce, za a bude taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ne a ranar 5 ga wata da safe, kuma za a rufe shi a ranar 13 ga wata, wato ke nan za a shafe tsawon kwanaki takwas ana taron. A gun wannan taron, za a saurari rahoton aiki da gwamnati za ta gabatar, sa'an nan za a duba wasu shirye-shirye da rahotanni na kasafin kudi da aka gabatar.

Kasancewarta hukumar koli ta kasar Sin wadda ke da ikon kafa dokokin kasar, majalisar ta wakilan jama'ar kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a kokarin da ake na zurfafa gyare-gyare. Madam Fu Ying ta ce, majalisar za ta ba da jagoranci ga gyare-gyare ta hanyar kafa doka. Ta ce, "ba da jagoranci ga gyare-gyare ta hanyar kafa doka shi ne a tsara dokokin da suka wajaba ko gyara su ko kuma yi watsi da dokokin da ba su dace ba a fannonin da suka shafi muhimman gyare-gyaren da ke jawo hankalin al'umma, don mu samu dokokin da muke iya bi wajen gudanar da gyare-gyaren."

An ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tuni ta tsara wani sabon shirin da ya shafi dokokin da za a kafa nan da shekaru biyar masu zuwa, wanda ya jibanci zaman al'umma ta fannoni daban daban, ciki har da tsara dokar kiwon lafiya da gyara dokar kiyaye ingancin abinci da kuma dokar kasafin kudi.

Batun kiyaye muhalli ya kasance batun da ya fi jawo hankalin al'umma a wajen taron. Tun farkon shekarar da muke ciki, matsalar gurbacewar iska ta rutsa da wasu manyan biranen kasar Sin. A game da haka, Madam Fu Ying ta bayyana cewa, gurbacewar iska tana ci wa wasu biranen kasar Sin tuwo a kwarya, kuma tana kara yaduwa zuwa wasu, don haka, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za ta gyara dokar kiyaye muhalli, don samar da tabbaci ga aikin daidaita matsalar gurbacewar iska. Ta ce, "majalisar wakilan jama'a ta fi sanya muhimmanci a kan kafa dokokin da suka shafi kiyaye muhalli, har ma ta fara aiki kan dokar yakar gurbacewar ruwa da dokar yakar gurbacewar kasa. Ban da haka, za mu fara duba yadda ake aiwatar da dokar yakar gurbacewar iska a wannan shekara, kuma bisa ga binciken da muka yi za mu gyara dokar."

Kafin taron, a madadin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Madam Fu Ying ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai wata tashar jiragen kasa da ke birnin Kunming a kudu maso yammacin kasar, kuma ta bayyana bakin cikinta game da mutuwar mutane a harin tare da jajanta wa wadanda harin ya rutsa da su. Ta ce, "Wadannan 'yan ta'adda ba su da imani, sun kashe duk wanda suka ga dama, muna yin Allah wadai da su da kakkausar murya, kuma muna bayyana bakin cikinmu kan mutuwar mutane a harin tare da yi wa wadanda har yanzu ke kwance a asibiti addu'a, muna fatan Allah ya saukaka musu. Baya ga haka, muna nuna jinjinawa ga 'yan sanda da kuma mutanen da suka nuna jaruntaka wajen artabu da 'yan ta'addan. Babu wata iyakar kasa da aka shata ga ta'addanci, don haka, muna fatan kasar Sin za ta iya samun hadin kai da fahimtar juna daga kasa da kasa a kokarin da take na yakar ta'addanci a nan gaba." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China