0304murtala
|
Shugabannin da za su jagoranci taron, kamar yadda sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim ya bayyana cikin wata sanarwa, ya ce su ne tsohon babban mai shari'a Dr. Idris Kutigi a matsayin shugaba, sai tsohon ministan harkokin cikin gida, Bolaji Akinyemi a matsayin mataimakin shugaba, yayin da kuma Dr. Valerie Azinge za ta kasance a matsayin sakatariya.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaban da sauran mataimakansa, za su kama aiki ne a ranar Larabar nan 5 ga watan Maris.
Sauran wakilai 492 da za su wakilci jama'ar kasar kuwa, za'a rantsar da su don fara ayyukansu a ranar 10 ga watan nan, kamar dai yadda shugaba Jonathan ya bayyana yayin tattaunawar da yayi kai-tsaye da manema labaran kasar a kwanan baya.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.