in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin harhada magungunan gargajiya na kasar Sin TASLY ya gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a Kano
2014-02-24 11:12:04 cri


A ranar Asabar 21 ga wata wani shahararren kamfanin harhada magungunan gargajiya daga kasar Sin mai Suna TASLY ya gudanar da wani taron wayar da kan ga abokanan hurdarsa dake birnin Kano a arewacin Najeriya.

Kimanin shekaru 8 ke nan kanfanin TASLY ya shafe a najeriya yana samar da ingantattun magunguna tsaftatattu kuma daga saiwoyi kala daban daban na gargajiya domin taimakawa wajan yakar cututtukan dake kawo nakasu ga rayuwar bil`adama.

A yayin taron karawa juna sanin da kanfanin na Tasly ya gudanar, babban manajan kasuwanci na kanfanin Mr. kang ya fara ne da bayyana samfurin magungunan da kamfanin nasu ke samarwa kamar su DANSHEN PILL wanda ake amfani da shi wajan samun sauki musamman a a yayin da kitse ya yiwa mutum yawa a jiki, jini baya gudanawa yadda yakamata.

Sauran sun hadar da DEEPURE TEA wanda ake amfani dashi a shayi, shi kuma yakan taimakawa mutum wajen samun sauki daga wata gajiya ko kuma ciwon jiki kamar dai yadda Mr. kang yayi mana Karin haske.

Suma wadansu daga cikin dillalan kamfanin na TASLY da suka halarci wannan bita sun bayyana yadda suka amfana daga abubuwan da aka sanar da su a wajen taron inda suka ce babu shakka daga yadda jama`a suka rungumi magungunan kamfanin, alamu sun nuna ana samun nasara sosai idan aka yi amfani da su.

A karshen taran an rarraba kyaututtuka na musmaman ga manya da kananan dillalan kamfanin na TASLY wadanda suka bayyana dumbun amfanin da suka dade suna samu daga magungunan da kamfanin ke samarwa.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China