in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rera wakokin wasan kwaikwayo na Beijing Opera a babban daki mai launin zinariya na birnin Vienna na kasar Austra
2014-02-24 17:55:44 cri

A 'yan kwanakin baya, a yayin da Sinawa suka taya murnar sabuwar shekara da bikin bazara a gida, a babban daki mai launin zinariya na birnin Vienna, mawaka da dama na kasar Sin sun rera wakokin wasan kwaikwayo na Beijing Opera don mika gaisuwa ga masu sauraro a ketare.

Mawaka masu suna Mei Baojiu, da Li Weikang, da Ge Qichang da dai sauransu sun hada kai da tawagar rera wakoki na kasa da ke birnin Vienna, inda suka nuna fasahohi masu kyau tare ga masu sauraro.

Ministan kula da harkokin zaman al'umma na kasar Austra Mista Rudolf Hundstorfer ya gaya wa manema labaru cewa, da wuya sosai a kalli wasan kwaikwayo na Beijing Opera a Turai, masu fasaha na Austra da mawaka da suka zo daga Beijing sun hada kansu da kyau, wannan ya burge ni sosai.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China