in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karo na farko shugaban kasar Sin ya zurfafa bayani kan babban makasudin gyare-gyare a dukkan fannoni
2014-02-18 16:43:10 cri

A ran 17 ga wata ne, a karo na farko babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya zurfafa bayani kan babban makasudin yin gyare-gyare a dukkan fannoni, ciki wani jawabi da ya gabatar a makarantar kwamitin tsakiya ta JKS, inda ya yi kira ga mahalartan taron da su kara kwarewarsu ta fuskar tafiyar da harkokin kasa bisa tsarin gurguzu da ke da halayyar musamman ta kasar Sin.

Cikakken taro na 3 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, wanda aka shirya a watan Nuwambar shekarar da ta shude, ya gabatar da wani babban shiri ga sabuwar hanyar da Sin take bi wajen yin gyare-gyare. A karo na farko, takardun da aka bayar a taron suka gabatar da babban makasudin zurfafa yin gyare-gyare a nan gaba, ciki hadda a kyautata tsarin gurguzu da ke da abubuwan musamman na Sin da raya shi, da zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kuma kwarewar yin hakan.

A ranar 17 ga wata, makarantar kwamitin tsakiya ta JKS ta shirya wani taron kara wa juna sani, wanda manyan ministoci da gwamnonin larduna suka halarta bisa babban takensa na 'zurfafa yin gyare-gyare a dukkan fannoni'. A jawabin da ya yi a wannan rana, Mista Xi ya zurfafa bayani kan babban makasudin yin gyare-gyare a dukkan fannoni. Ya ce,

'Dole ne mu saba da babban yunkurin zamanintar da kasa, da inganta kwarewar JKS wajen tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata, da kuma aiwatar da dimokuradiyya, da murtaba dokoki, da kuma kara daga kwarewar hukumomin gwamnati wajen aiwatar da ayyukansu, da kuma inganta kwarewar jama'a wajen kula da harkokin kasa, sai kuma harkokin inganta zamantakewar al'umma da al'adu, da harkokinsu na yau da kullum, da kuma cimma burin tafiyar da harkokin JKS, da kasa, da jama'a bisa tsari, da bin ka'idoji da shirin da aka tsara, da kara kwarewa ta tafiyar da harkokin kasa bisa tsarin gurguzu da ke da abubuwan musamman na Sin.'

Mista Xi ya karfafa cewa, tsarin tafiyar da harkokin kasa da aka zaba yana da nasaba da gargajiya a tarihi, da al'adun al'umma, da matsayin da ake ciki dangane da tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma, kamar yadda jama'ar kasa suka zabi hakan. Tsarin tafiyar da harkokin kasar Sin yana bukatar yin gyare-gyare, amma yaya za a yi gyare-gyare, ya kamata mu dage bin ra'ayinmu da kyakkyawar niyya. Ya ce,

'Kabilar Sin wata kabila ce da ta kan yi koyi daga waje, a tarihi, ta kan koyi kyawawan abubuwa na saura, don su zama nata, sa'an nan kuma kabilar Sin ta samu abubuwan musamman nata. Idan ba mu da imani kan tsarinmu, to, za mu rasa karfin zuciya na yin gyare-gyare, bugu da kari kuma, idan ba mu yi gyare-gyare ba, to, ba za mu rike da kyakkyawan tsarinmu ba. Dalilin da ya sa muke yin gyare-gyare a dukkan fannoni shi ne, sabo da muna son kara kyautata tsarin gurguzu da ke da abubuwa na musamman namu. Muna da imani kan tsarinmu, ba wai ba za mu canza ba, a'a, za mu kara yin gyare-gyare, don tsarinmu ya kara samun ci gaba.'

Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa, yin gyare-gyare ayyuka ne da aka yi bisa matakai daban daban, ya kamata mu samu niyyar canzawa, haka kuma za mu yi hakan bisa matakai a kai a kai, don tabbatar da cimma burin babban makasudin yin gyare-gyaren. Ya ce,

'An tsara ayyukan yin gyare-gyare ne bisa babbar moriyar kasa, da moriya ta nan gaba, bai kamata a ki gudanar da sauyi ba, muddin akwai bukatar hakan. Idan wani abu yana da amfani ga sha'anin JKS da jama'a, wanda kuma yake iya samar da moriya ga jama'a, da kuma samar da ci gaba a dogon lokaci ga JKS da kasar Sin, to, ya wajaba mu aiwatar da shi, kuma mu yi gyare-gyare idan akwai bukata.'(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China