in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kira taro karo na biyu don tabbatar da tsaftacacciyar gwamnati
2014-02-12 17:03:52 cri

A ran 11 ga watan Fabrairun nan ne majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ta kira taro karo na biyu don zakulo hanyoyin tabbatar da kafuwar tsaftacacciyar gwamnati a kasar.


Yayin taron zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma firayin ministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya karfafa cewa, ainihin iko ga gwamnati shi ne, nauyin dake wuyanta na ba da hidima ga jama'a. Ya ce kamata ya yi a aiwatar da manufofin da kwamitin tsakiya na JKS ya gabatar, wajen tabbatar da tsaftacacciyar gwamnati, wato a bi dokoki, a haramta abubuwa da suka saba wa dokoki, a kuma yi yaki da ko wane irin yanayi na cin hanci da rashawa, tare da gurfanar da masu laifuffuka gaban shari'a.


Tun farkon kafuwar da wannan gwamnti a watan Maris na shekarar da ta wuce ne dai, firaminista Li Keqiang ya gabatar da abubuwa uku ga majalisar gudanarwa, wato a cikin wa'adin aiki na wannan gwamnati, gwamnati ba za ta ci gaba da gina sababbin gine-gine da dakuna iri na gwamnati ba, ba za ta kara shigar da ma'aikata zuwa gwamnati ba, a maimakon haka za ta rage yawansu, haka kuma gwamnati ba za ta kara yawan kudin hidimar bakunta, da na ziyara a ketare ba. Ya ce za kuma a rage yawan kudin da ake kashewa wajen sayen motoci.

A gun taron karo na biyu don tabbatar da kafuwar tsaftacacciyar gwamnati, Mista Li ya bukaci sassan gwamnati, da daukacin hukumomin ta, da su ci gaba da aiwatar da manyan manufofin tsaftace ayyukan hukuma guda 8, da abubuwa uku ga majalisar gudanarwa.

'Sababbin gine-gine da dakuna irin na gwamnati, ba za a ci gaba da ginawa ba, idan an saba wa hakan, ta ko wace irin hanya, lallai za a zartas da hukunci. Za a kayyade yawan hukumomi da ma'aikatan gwamnati a tsanake, ba za a iya saba wa hakan ba. Ban da wannan kuma, za a ci gaba da sarrafa kudin da ake kashewa wajen kula da bakunta da na tarurruka, ba za a kara yawan kudin ba, hasali ma dai za a rage shi ne. Idan gwamnati ba ta kashe kudi da yawa ba, za a iya yin amfani da kudin da suka yi rara wajen kyautata zaman rayuwar jama'a, da bunkasa ayyukan jin dadin jama'a.'

Game da aikin kafa muhimmin tsari na yaki da cin hanci da rashawa, da tabbatar da tsaftacacciyar gwamnati, Mista Li Keqiang ya ce, za a kafa tsarin yin rajistar kadarori, za a kyautata hanyar da gwamnati take bi wajen ba da kudi, don warware matsalar samun kudi ba bisa doka ba.

'A bana, za mu mai da hankali kan tsari, za mu kyautata tsarin da a kan samu matsalar cin hanci da rashawa cikin sa, za a tabbatar da ka'idoji, da dokoki yayin da gwamnati take aikin bayar da tanda, da sayen kayayyaki, da ikon amfanin da gonakan kasa, da ikon sayar da ma'adinnai da dai sauransu.'

Mista Li ya bayyana cewa, ya kamata a kayyade kudin gwamnati, tare da sa ido yadda ya kamata, game da masu karya dokoki kuwa, ya ce hukumomin bincike da sa ido ba za su ji tsoro ba, za su ci gaba da yin bincike yadda ya kamata. Ya ce,

'Ya kamata a kula da dukkan kudaden da gwamnati ta samu, da wanda ta kasha bisa shirin da aka tsara, wato a tsara shirin kula da kudin da gwamnati ta samu, da shirin kula da kasafin kudi, da kuma wani shirin musamman na kula da kudin da gwamnati ta kashe. Ya kamata a kayyade ma'aunin aikin akanta, domin tabbatar da amfani da kudin gwamnati yadda ya kamata, za a dudduba, da sa ido kan dukkan aikin da ya danganci kudin gwamnati, da kadarorin gwamnati, da ma'addinan gwamnati.'

Mista Li ya bukaci a sa kaimi ga tafiyar da harkokin gwamnati a fili, ya ce ya kamata a bayyana dukkan kudaden da gwamnati take amfani da su wajen lura da bakunta, da sayen motoci, da ziyara a ketare, ba tare da wani boye boye ba.

'Game da abubuwa dake da nasaba sosai da moriyar jama'a, wadanda suka hada da lafiyar abinci da magunguna, da kebe dakunan lura da jama'a mafi talauci, da kudin hidima na likitanci, da shigar da dalibai cikin jami'o'i, da shigar da ma'aikata cikin hukumomin gwamnati da kamfanoninta, da dai sauransu, za a bayyana su a fili.'(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China