in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin nuna wasan kwaikwayon Sinanci "Doudou da surukanta" a Gabon
2014-02-08 14:46:49 cri

A ranar Jumma'a 7 ga wata ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Gabon da gidan telebijin na Gabon suka shirya wani kasaitaccen bikin fara nuna wasan kwaikwayon Sinanci mai taken "Doudou da surukanta" tare a babban dakin nune-nunen gidan telebijin. Manyan jami'an ma'aikatar kula da harkokin yada labaru ta Gabon, da ma'aikatar al'adun kasar da masu harkar fina-finai da 'yan jaridu da wakilan kamfanonin kasar Sin da ke wurin sama da 150 ne suka halarci bikin bisa gayyatar da aka yi musu.

Shugaban gidan telebijin na kasar Gabon Meansa ya yi jawabi cewa, nuna fina-finan Sinawa a kasar Gabon ba ma kawai zai kawo nishadi ga jama'ar kasar ba, har ma zai samar da wani dandalin sanin al'adun Sinawa. Yana fatan fina-finan kasar Sin za su karade gidajen al'ummar kasar, kuma za su kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.

A jawabin fatan alheri da jakadan Sin a kasar Gabon Sun Jiwen ya gabatar, ya ce, nuna wasan kwaikwayon "Doudou da surukanta" a kasar Gabon, ya kasance wani babban batu cikin mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasashen biyu. Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya da ke tsakanin kasashen Sin da Gabon, kasashen biyu za su shirya wasu bukukuwan al'adu domin murnar wannan rana mai muhimmanci. Nuna wasan kwaikwayon "Doudou da surukanta" ya zama biki na farko da aka shirya dangane da zagayowar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, kana babbar tsaraba ce da kasar Sin ta baiwa jama'ar Gabon, yana fatan jama'ar Gabon za su ci gaba da mai da hankali game da bubukuwan al'adun kasar Sin da za a shirya nan gaba, don jin dadin abubuwan dake kunshe a ciki.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China