in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka: nahiyar da matasan Sin suke son fara ayyukansu
2014-02-07 17:31:18 cri

A halin yanzu ana samun karin matasan kasar Sin da suka tafi nahiyar Afirka da mai nisa sosai daga kasar Sin, inda suke son raya ayyukansu da kuma zaman rayuwarsu, sakamakon karin mu'ammala da hadin gwiwa da ake yi tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin cikin 'yan shekarun nan da suka gabata. Wasu daga cikin wadannan matasa sun fara ayyukansu a kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka bayan kammala karatunsu daga jami'o'i, wasu daga cikinsu sun taba samun ayyuka masu kyau da kuma zaman rayuwa mai inganci a kasar Sin, amma sun je Afirka don fara sabbin ayyuka. Harkokin da suka yi da kuma mutanen da suka hadu da su a kasashen Afirka dukkansu sun kara ma wadannan Sinawa fahimta game da nahiyar da al'ummarsu sosai, kuma a halin yanzu, matasan kasar Sin suna son fara ayyukansu a wannan nahiyar ta Afirka. Sakamakon karuwar mu'amala a tsakanin matasan kasar Sin da kasashen Afirka, matasa da dama na kasashen Afirka suna sha'awar harkokin kasar Sin. Yanzu bari mu sauraro rahoton da wakilan Gidan Rediyommu CRI suka kawo mana:

A watan Nuwamba na shekarar 2011, malama Zheng Ying mai shekaru 23 wadda ta ajiye aiki a wani kamfanin a nan kasar Sin, ta tafi yawon shakatawa a kasar Zambia, amma bayan 'yan watanni da ta zauna a nahiyar Afirka, gaskiya, zaman rayuwa a nahiyar Afirka ta burge ta sosai, shi ya sa, ta tsai da kudurin cewa, za ta ci gaba da zamanta a Afirka, kuma za ta fara sabon aikinta a nahiyar. Don haka a karshen wannan shekara, ba ta koma kasar Sin don bikin sabuwar shekara ta gargajiya tare da iyalinta ba, sai ma ta tafi kasar Tanzania, ta fara aikin ba da jagoranci ga masu yawon shakatawa a kasar. Bayan shekaru biyu da kasancewarta a kasar Tanzania, ta kafa wani kamfanin yawon shakatawa tare da wasu abokanta. Malama Zheng Ying yarinya ce mai hankali da kuma sanin ya kamata, dalilin haka kuwa in ji ta, "zaman rayuwata a Afirka ta kara mini ilimin zaman duniya sosai", in ji malama Zheng Ying.

Zaman rayuwar nan na da sha'awa sosai, kuma ta sa mini samun 'yanci, a halin yanzu, idan akwai lokaci, ina son in tafi yawon shakatawa a sauran kasashen Afirka, da farko ina son in je neman visa na kasa wadda nake son tafiya, sa'an nan kuma na dukufa wajen kara fahimta ta game da wurin da zan je yawon shakatawa, bayan na shirya, sai in tafi. Bugu da kari, na samu abokan arziki da dama a Afirka, ciki har da wasu tsofaffi wadanda suka dade suna zaune a Afirka, na koyi abubuwa masu daraja da dama sosai daga wajensu, idan ba don dalilin haduwarmu da ba zan iya koyon wadannan abubuwa ba, idan da ban tafi Afikra ba, da na kasance karkashin kulawar iyayena a kasar Sin.

Ban da malama Zheng Ying, akwai matasa da dama wadanda suka tafi Afirka don kara sani da kuma cimma nasarorin ayyukansu. Malam Zhang Renquan wanda a halin yanzu yake aiki a kamfanin shimfida layukan dogo na kasar Sin (kamfanin Railway Construction Engineering na kasar Sin) dake Zanzibar, a da fatansa shi ne ya zama ma'aikacin gidan jarida, amma sabo da wasu dalilai bai iya cika fatansa ba. A shekarar 2013, bayan ya kammala karatunsa a jami'a, ya sami wata damar aiki a Afirka, ba tare da bata lokaci ba, ya karbi wannan aiki, wanda ya sa ya tafi Zanzibar. Ko da yake ya hadu da matsaloli da dama a Zanzibar, amma ya bayyana cewa, gaskiya ya taki sa'a sosai dangane da abubuwa da ya ci karo da su a wannan tsibirin:

Na ga abubuwa da yawa a Afirka, kuma na kara fahimta sosai game da zama rayuwa, shi ya sa, akwai abubuwa da dama da nake son in rubuta, a ganina, sabo da abubuwan da na fuskanata a rayuwa ta da na zo Afirka sun yi bamban da na sauran mutane, abubuwan da na rubuta ba za su yi kama da na sauran mutane ba, babu shakka za su kasance abubuwa masu ban sha'awa. Idan bayan shekaru da dama, na iya samun wata dama na yin aikin dan jarida, ina da imani cewa, abubuwan da zan rubuta, kuma hotunan da zan dauka, dukkansu za su yi bambanta da nake yi a halin yanzu, sabo da mutane da abubuwan da na hadu da su a Afirka sun sa na kara fahimtar zaman rayuwa sosai. Gaskiya, akwai abubuwa masu yawa da matasa za su iya yi a nan duniya, musamman ma a Afirka, kuma za a ci gaba da samun abubuwan da matasa za su iya kirkirowa a nan gaba. Shi ya sa, a rayuwata, na samu damar yin aiki a nan, abun alfahari ne kuma babban sa'a ne sosai gare ni.

Ko da yake wadannan matasa sun sha wahala musamman na kewan gida, bayan zamansu a kasashen Afirka na shekaru da dama, sun samu abokai da yawa, wasu kuma sun zo ne daga kasar Sin, wasssu kuma 'yan Afirka, wannan ya sa, sun samu saukin wahalarsu na jin kewan garuruwansu. Har ma, domin mu'amalar da suke yi, wasu abokan nan su 'yan Afirka sun fara sha'awar harkokin kasar Sin.

"Akwai tsibirai guda biyu a Zanzibar, watau tsibirin Zanzibar da kuma tsibirin Pemba. Zanzibar tana kudancin ikwaitar duniya, yanayin zafi mafi yawa a yankin ya kai makin digirin Celcius 38, yayin da yanayin sanyi mafi yawa ya kai makin digirin Celcius 28, gaba daya muraba'inta ya kai kimanin kilomita dubu daya da dari bakwai, kuma yawan mutane ya kai dubu dari shida. Zaman rayuwa a Zanzibar na da dadi sosai, kuma ana da kayayyaki da wuraren tarihi da dama a nan……"

Karkashin zafin ranar ikwaita, Salima Ali Saleh tana amfani da Sinanci wajen bayani ga masu yawon shakatawa wadanda suka zo daga kasar Sin game da harkokin Zanzibar, malama Salima ita ce 'yar Zanzibar, wadda ta taba zuwa kasar Sin don koyon wasan Kung Fu na watanni 6, inda ta samu sunanta na Sinanci "Xia Lin", tana jin dadin wannan suna sosai, kuma ta fi son masu yawon shakatawa daga kasar Sin su kira ta da wannan suna. Bayan da ta koma kasarta daga kasar Sin, ta yi aikin mai horas da fasahar wasan Kong Fu, a sa'i daya kuma tana aikin mai bada jagoranci ga masu yawon shakatawa, sana'ar da ta sa ta yi suna sosai cikin wadannan tsibirai biyu, sabo da masu iya Sinanci a cikinsu ba su da yawa a Zanzibar.

Idan aka kwatanta da malama Xia Lin, malam Mwatula Chiti wanda a halin yanzu ke aiki a bankin kasar Sin dake kasar Zambia, ya fi dadewa wajen zama a kasar Sin, ya taba yin karatu a jami'ar koyon ilmin sha'anin kudi da tattalin arziki na kasar Sin na shekaru biyar, har yanzu bai manta da zamansa a kasar Sin ba, dukkan mutane da ya hadu da su ko kuma harkokin da ya yi a kasar Sin sun burge shi sosai, shi ya sa, ya rubuta wata waka da kansa don nuna kaunarsa ga birnin Beijing na kasar Sin yayin da yake karatu a Beijing, ya kuma rera wannan waka a yayin bikin taya murnar sabuwar shekara da kamfaninsa ya shirya a shekarar bana:

"Ni ne dan Beijing, ni ba bako ba ne, shekaru biyar na zauna a nan Beijing, amma har yanzu kana kira ni bako, ko wane rana kuna gani na, amma har yanzu kuna kira ni bako, me kuke nufi? Wallahi, abin da mamaki! Ina son iyayena su zo Beijing tare da ni, ina son su ji dadin zaman rayuwa tare da ni a nan Beijing, ni ba mai yawon shakatawa ba ne, ka fahimce ni? Ina jin dadin zama rayuwata a nan birnin Beijing, ina farin ciki sabo da ina nan a birnin Beijing, kuma Beijing yana nan cikin zuciyata."

Sabo da ci gaba da karuwar mu'ammala da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a halin yanzu, matasan kasar Sin masu yawa suna son zuwa nahiyar Afirka don fara ayyukansu, kuma matasan Afirka suna ci gaba da kara sha'awarsu game da kasar Sin cikin 'yan shekarun nan, babu shakka a nan gaba, matasan kasashen Sin da Afirka za su kai inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon matsayi.

To, masu sauraro shirinmu na yau ke nan, shi ne kuma bayanin karshe da sashen Hausa na CRI ya shirya muku dangane da huldar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a cikin makonni biyu da suka gabata. Muna fatan kun amfana, a madadin Maryan da ta shirya muku shirin, ni Fatimah Jibril da na gabatar ke cewa ku huta lafiya daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin CRI.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China