in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudumawar da likitocin kasar Sin ke bayarwa ga marasa lafiya a yankin Zamzibar
2014-02-06 15:28:09 cri

Ran 12 ga watan Janairu na shekarar ta 2014 rana ce ta cika shekaru 50 da samun nasarar juyin juya halin a Zanzibar. A yayin bikin da aka shirya don murnar zagayowar wannan rana, an gayyaci likitocin kasar Sin wadanda suke aiki a tsibirin Zanzibar da su halarci bikin a matsayin manyan baki. Wannan ya bayyana cewa, gwamnati da al'ummar kasar suna nuna girmamawa sosai ga kungiyar likitocin kasar Sin da suka shafi shekaru 50 suna aiki a yankin, kuma suke nuna tausayinsu kwarai ga jama'ar yankin. Yanzu ga wani bayanin da wakilanmu suka aiko mana.

A cikin asibitin Mnazi Mmoja dake tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania, wata yarinya mai suna Chikujuma Khaudja wadda ta kamu da lalurar shanyewar bangaren fuskarta tana samun jiyyar allurar zurfa da wani likitan kasar Sin ke yi mata, ta gaya wa wakilinmu cewa, ta shafe watanni biyar tana zuwa asibitin sau biyu a kowane mako, kuma ta tsaya kan shan maganin da likitan kasar Sin ya ba ta. Ya zuwa yanzu ta samu sauki sosai. Khaudja ta ce, "Kafin na zo nan, iyayen sun ce likitocin kasar Sin ba za su iya warkar da wannan ciwo ba. Amma yanzu sun ga na samu sauki sosai, sai suka fara amincewa da fasahar likitan kasar Sin. Idan da ba don likitocin kasar Sin, ban san yaya zan yi. Mai yiyuwa ne na je na nemi taimako daga wajen likitan gargajiya na wurinmu. Ba abin da za su iya yi, illa su ja fuskata da karfi kwarai, kuma zan ji zafi kwarai."

A yankin Zanzibar, mazauna wurin su kan je asibitin dake da likitocin kasar Sin ne kamar yadda Khaudja take yi.

Yankin Zanzibar yana kunshe ne da tsibirin Zanzibar da na Pemba, yankin ya yi kama da wani lu'ulu'u mai kyaun gani dake kan tekun Indiya. Sai dai ya kasance yanki mafi fama da talauci a duk duniya a idon M.D.D.. Sakamakon haka, mazauna wurin da likitocin kasar Sin wadanda suke zaune tare da yin aiki a wurin suna shan wahala sosai. Wata rana, bututun ruwa dake sansanin likitocin kasar Sin ya fashe. Sabo da ba a iya gyara shi kamar yadda ake fata ba, ba su da wata hanyar da ta rage, sai su sayi ruwan sha mai tsada kwarai. Sakamakon haka, ba su iya wanke fuska da hannu da kafa kamar yadda suka saba yi ba.

Ba ma kawai suna shan wahala sosai a cikin zaman rayuwarsu ba, har ma suna ganin abin mamaki sosai ga yanayin jiyya a wurin. Mr. Xie Yunliang, karamin jakadan kasar Sin dake yankin Zanzibar ya ce, wata maganar da ministan kiwon lafiya na yankin Zanzibar ya gaya masa ta burge shi ainun.

"Na tambayi ministan likitoci nawa suke aiki a Zanzibar? Ya ce, akwai likitocin kasar Sin guda 20, likitocin Cuba guda 14, sannan akwai likitociin Zanzibar guda 25 kawai. Na dauka cewa, ko ban ji sosai ba? Na sake tambayarsa cewa, mutane miliyan 1 da dubu dari 3 wadanda suke zaune a tsibirai guda 2 suna da likitoci 25 kawai? Ya ce, e, haka ne, akwai likitoci 25 ne kawai."

Sinawa su kan ce, idan kana son taimakawa kasashen Afirka, ya kamata ka samar musu abubuwan da suke bukata cikin gaggawa. Sabo da haka, tun daga shekarar 1964, kasar Sin ta soma aika likitoci zuwa Zanzibar, kuma ba a daina yin hakan ba a cikin shekaru 50 da suka gabata. A 'yan shekarun nan, bisa hakikanin yanayin da ake ciki a Zanzibar, kungiyar likitocin kasar Sin ta kafa "cibiyar murmushi", "cibiyar endoscope", "cibiyar kawar da yanar ido" da "cibiyar kawar da ciwon ciki". Sannan a watan Disamba na shekarar 2013, kungiyar likitocin kasar Sin ta kaddamar da "cibiyar kula da kashi" a tsibirin Pemba.

Tsibirin Pemba na daya daga cikin yankuna mafi muhimmanci wajen fitar da citta mai kamshi a duk duniya. Irin wannan nau'i na citta yana da muhimmanci sosai ga tattalin arzikin yankin Zanzibar. Amma akwai hadari sosai wajen tsintar cittar, idan ba a mai da hankali sosai ba, ana iya fadowa daga dutse mai tsayi sosai. Sakamakon haka, mutane da yawa, musamman yara su kan fado, har su karye. Sabo da haka, Mr. Mkasa, ministan kiwon lafiya na Zanzibar ya yi farin ciki sosai da kaddamar da cibiyar kula da kashi.

"Yau, mun zo nan ne domin mu kaddamar da wannan cibiya wadda take da muhimmanci ga mazauna tsibirin Pemba. A da, sai mun kashe kudi da yawa kafin mu kai marasa lafiya zuwa asibitin Dares Salam dake babban yankin Tanzania. Yanzu, za su iya samun jiyya a tsibirin."

Ba ma kawai kungiyar likitocin kasar Sin sun je yankin Zanzibar tare da kayayyakin asibiti, da kuma kafa hukumomin aikin jiyya ba, har ma sun yi kokarin horar da likitocin wurin.

Likita Liu Hualian wanda ya kware sosai wajen aikin tiyata kan ciwon tsagar lebe da ganda ya taba duba wata maras lafiya mai shekaru 32 da haihuwa. Lokacin da ya dace na yi mata tiyata, shi ne tun tana karama, sakamakon haka, ya nuna cewa, ta wuce lokacin da ya dace. Wannan mata ta ce, lokacin da take karama, iyayenta ba su da kudi, sabo da haka, aka yi mata aikin tiyata a ciwon lebe kawai, ba a gyara gandan ba. Amma yanzu bayan da likita Liu na kasar Sin ya yi mata aikin tiyata, tana iya cin abinci kamar yadda sauran mutane suke yi. Wata rana, ta bai wa likita Liu wai anbulan. Mr. Liu ya ce, "A kwanan baya, yayin da na isa dakin ganawa da marasa lafiya, sai ta zo wajena, ta ba ni wani anbulan, wannan ya tsorata ni. Na tambaye ta me take nufi? Ta ce, kyauta ne take son ba ni. Na gaya mata cewa, bai kamata ta yi haka ba. Ta yi dariya, ta bude wannan anbulan din ta nuna mini cewa wata wasikar nuna godiya ce kawai. Ta ce, idan da kungiyar likitocin kasar Sin ta kaddamar da wannan cibiya da wuri, da ba ta jira har wannan lokaci ba."

Wannan magana ta burge likita Liu da takwaransa na kasar Sin. A shekaru 60 na karnin da ya gabata, Zhou Enlai, wato firaministan gwamnatin kasar Sin na wancan lokaci ya taba karfafa gwiwa ga kungiyoyin likitocin kasar Sin cewa, bai kamata su ceci marasa lafiya kawai ba, ya kamata su yi kokarin horar da wasu likitocin wurin. Yanzu, akwai wani kwalejin koyon ilmin likitanci a yankin Zanzibar, amma babu littattafan koyon ilmin kawar da ciwon lebe da ganda, balle likita. Sabo da haka, idan likitocin kasar Sin suka gama aiki da rana, sai su yi amfani da lokacin da suke da shi da dare su rubuta wani littafin koyon ilmin kawar da ciwon lebe da ganda cikin harshen Turanci, kuma za a wallafa shi nan ba da jimawa ba.

A cikin shekaru 50 da suka gabata, kungiyoyin likitocin kasar Sin sun ba da gudummawa sosai ga kasashen Afirka da Latin Amurka da Asiya masu fama da talauci. Yanzu gwamnatin kasar Sin na tunanin yaya za a iya kara kyautata ingancin ba da jiyya a wadannan kasashe wadanda suke karbar kungiyoyin likitocin kasar Sin. Mr. Ren Minghui, direktan hukumar kula da harkokin hadin gwiwa ta ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Muna fatan a nan gaba za mu iya zabar wasu kasashe ko yankuna a Afirka, ta yadda za mu iya kafa wasu cibiyoyin kasar Sin na koyon ilmin likitanci, mai kunshe da sashen koyar da ilmin likitanci, da asibiti da kuma sashen nazarin ilmin likitanci. Za mu iya kafa su ne ta hanyar yin hadin gwiwa, ko ta hanyar kasuwanci. Bugu da kari, za a iya koyar da ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin a cikin irin wadannan cibiyoyi, ta yadda za a iya ba da hidima mai kyau ga jama'ar kasashen Afirka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China