140214-bikin-yuanxiao-danladi
|
Yanzu Sinawa sun ji murna sabo da sabuwar shekara bisa kalandar kasar Sin, kowa da kowa na je gidajensu don taru da iyalansu da dangogi. A cikin shirinmu na da, mu riga mu tattauna kan yadda Sinawa suke jin dadin sabuwar shekara. Bayan bikin sabuwar shekara, bari mu ga wani bikin daban a makonni biyu bayan ranar sabuwar shekara bisa kalandar Sin, wato bikin Yuanxiao.
Bikin Yuanxiao bisa kalandar kasar Sin, yana daya daga cikin bukukuwan gargajiya na kasar Sin wanda kuma yake kawo karshen duk bikin bazara.
Bikin Yuanxiao ana kiran shi bikin Yuanxi, bikin Yuanye ko kuma bikin Shangyuan. Ranar bikin Yuanxiao na daren farko a daidai tsakiyar watan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya. A wannan dare, jama'ar kasar Sin su kan gudanar da al'adar rataya fitilu masu launi iri- iri, dalilin da ya sa ake shi bikin Yuanxiao da sunan "bikin fitilu".
Ina kallon fitilu da cin wani nau'in abincin da ake kira Yuanxiao, wadannan sun kasance muhimman abubuwa guda 2 da akan yi a lokacin bikin Yuanxiao. Me ya sa akan rataya fitilu a gun bikin Yuanxiao? An ce, a shekarar 180 ta kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam, sarkin daular Xihan ta kasar Sin wato sarkin Hanwendi ya hau karagar mulki a ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar kasar Sin. Domin murnar wannan hawan sarauta, sarkin ya tsai da kudurin kebe wannan rana a matsayin ranar bikin nunin fitilu. A wannan rana da dare ta kowace shekara, sarkin ya kan fita daga fadarsa domin yawon shakatawa, yana murna tare da jama'a. A wannan rana kuma, a kowane gida da kuma kan tituna manya da kanana akan rataya fitilu masu launi kuma masu ban sha'awa iri daban-daban domin mutane su je su kalla. Zuwa shekarar 104 ta kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisallam, an tsai da bikin Yuanxiao da ya zama wani muhimmin bikin kasar Sin a hukunce. Kudurin ya kara habaka sikelin bikin Yuanxiao.(Danladi)