in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata masana'antun kasar Sin su nuna sanin ya kamata yayin da suke zuba jari a kasashen Afirka
2014-02-05 15:27:03 cri

Bisa tanade-tanaden da ke cikin takardar yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya da gwamnatin Sin ta kaddamar a shekarar 2013, an ce, yanzu nahiyar Afirka ta kasance kasuwar ba da kwangilar aiki ta biyu ga kasar Sin kuma ta hudu a matsayin samun jarin da kasar Sin ta zuba. Karin masana'antun kasar Sin sun je kasashen Afirka domin samun zarafin kasuwanci. Amma wasu sun gamu da wasu matsaloli, alal misali masana'antun kasar Sin da yawa sun shiga wata kasuwa a lokaci guda.

Yanzu masana'antun kasar Sin sun kara mai da hankali kan nahiyar Afirka, don haka takarar da ke tsakaninsu a Afirka ta tsananta. Kamfanin kula da ayyukan yin amfani da ruwa da samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa na kasar Sin wato Sinohydro ya samu kwangilar fadada tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa mafi girma a kasar Zambiya, duk da haka a ganinsa, yana fuskantar matsin lamba. Liu Benjiang, babban darektan sashen kamfanin a kasar Zambiya ya gaya mana cewa,"A da kamfaninmu ne shi daya tak a nan kasar Zambiya a matsayin kamfanin da ke karkashin gwamnatin kasar Sin. Amma ina tsammani, yanzu kamfanonin gwamnatin kasar Sin a kalla 6 ne a nan, sun yi yawa sosai. Takarar da ke tsakaninmu ta tsananta. Yawan masana'antun sun fi karfin kasuwar Zambiya"

Kamar yadda mista Liu Benjiang ya fada, Zhou Jianjun, babban darektan sashen bankin kasar Sin a kasar Zambiya shi ma yana dan damuwa. Bayan da bankin kasar Sin ya kaddamar da reshensa a kasar Zambiya, yana samar wa masana'antu da dama hidimomin kudi. Zhou Jianjun ya ce, yanzu yawan masana'antun kasar Sin fiye da kima ya zama wata babbar matsala ga masana'antun kasar Sin da ke yin cinikayya a wurin. Zhou ya ce,"A baya, idan gwamnatin kasar Zambiya ta tallata wani aiki, kullum masana'antu guda biyu ko uku ne kawai su kan shiga neman kwangilar, amma yanzu yawan masu neman a ba su aikin ya ninka sau 10 ko fiye da haka. Masana'antu da yawa sai karuwa suke yi a kasar Zambiya."

Karuwar yawan masana'atun kasar Sin a kasashen Afirka ta haifar da takara, amma wasu masana'antun kasar Sin sun mai da hankali kan harkokin kasuwancin da za su iya samu a Afirka kawai, ba sa yin la'akari da barazarar da mai yiwuwa za su fuskanta a wurin .Mista Zhou Jianjun ya kara da cewa,"A duk lokacin da gwamnatin kasar Zambiya ta tallata manyan ayyuka, takarar da ke tsakanin masana'antun kasarmu kan yi kamari. Sannan ba sa yin la'akari da barazarar da za su fuskanta bayan samun kwangilar. Alal misali, gwamnatin kasar Zambiya tana fama da babbar matsalar gibin kasafin kudi, ta kan fuskanci matsalar biyan kudi. Bayan da muka samu kwangilar, kana muka kammala aiki yadda ya kamata, yanzu maganar ita ce ko za a biya mu kudin aikinmu ko a'a ita ce barazanar."

Karuwar yawan masana'antun kasar Sin a wuri guda kan kawo dukkan masana'antun kasar Sin da ke wurin babbar illa. Zhou Jianjun ya yi bayani da cewa,"Hakika kasuwar ba ta da girma sosai a nan Zambiya. Karuwar yawan masana'antun kasar Sin fiye da kima ta haddasa rudani a kasuwar, lamarin da ya kawo cikas ga takarar da ke tsakanin masana'antun kasar Sin."

Ban da takarar da ba ta dace ba da ke tsakanin masana'antun kasar Sin, wasu sabbin masana'antu ba su san dokoki da kuma al'adun gargarjiyar wurin sosai ba, don haka su kan haifar da sabani a tsakaninsu da sassa daban daban na wurin. Chai Zhijing, mashawarcin jakadan kasar Sin ta fuskar tattalin arziki da ke kasar Zambiya ya bayyana cewa,"Masana'antun kasar Sin sun kware a fannonin gudanar da ayyukan gine-gine da tattara kudi, amma suna bukatar kyautata kwarewarsu ta fuskar zuba jari. In suna son zuba jari a wata kasa, to, ya zama tilas su yi nazarin kwarewar gwamnatin kasar da makomarta, su yi la'akari da yadda ake tafiyar da manufofin kasar, da yadda za su yi cudanya da masana'antun wurin, mazauna wurin, da kungiyoyin wurin ta fuskar addini, harkokin 'yan kwadago da makamantansu."

Habaka cinikayya a ketare da masana'antun kasar Sin suke kokari a kai a halin yanzu yana taimakawa wajen raya masana'antun su kansu, haka kuma yana iya tabbatar da samun nasara tare a tsakanin masana'antun da sassa daban daban na wurin. Amma idan yawan kwararar masana'antun kasar Sin a wuri guda ba tare da sanin ya kamata ba ta kan lalata moriyar masana'antun, tare da kawo illa ga kimarsu a wurin. Ba a kasar Zambiya kawai ba, irin wannan abu yana faruwa ma a kasashen Tanzaniya, Mozambique da sauran kasashen Afirka. Ainihin dalilin da ya sa haka shi ne domin kafin wasu masana'antun kasar Sin su shiga wata kasa, ba sa yin bincike kan kasuwar kasar daga dukkan fannoni. Dangane da haka, Xie Yunliang, karamin jakadan kasar Sin da ke Zanzibar ya nuna cewa, kafin masana'antun kasar Sin su yi shirin habaka cinikayya a kasashen Afirka, ya zama tilas su yi bincike kan kasuwannin wurin daga dukkan fannoni, su zuba jari bisa sanin ya kamata. Mista Xie ya ce,"Idan kana son samun nasara, to, dole ne ka kara fahimtar abubuwan da suka kamata ka lura da su, ka zabi bangaren da ya dace a zuba jari a kansa, ka kara sanin albarkatun da za ka iya yin amfani da su a wurin da kuma dokokin wurin."

Shi ma Zhou Jianjun, babban darektan sashen bankin kasar Sin a kasar Zambiya ya jaddada cewa, bayanan da suka shafi tarihi ya sa aka kara kyautata dokoki sosai a kasashen Afirka, don haka kafin masana'antun kasar Sin su shiga kasashen Afirka, baya ga kara saninsu kan kasuwannin wurin, ya zama tilas su kara fahimtar dokoki wurin domin kaucewa fuskantar duk wata matsala ko barazana. Zhou Jianjun ya ce,"Kasashen Afirka sun sha bamban da juna a fannin tsarin siyasa. Kafin masana'antun kasar Sin su fara yin cinikiyya a wurin, ya zama dole su kara sanin dokokin wurin. Hakika dai, dokoki sun kyautata sosai a kasashen Afirka. Akwai dokoki masu yawan gaske a wurin da ya kamata kowa ya bi. Idan sun fahimci halin da kasashen Afirka suke ciki bisa yadda suke tafiyar da harkokinsu a kasar Sin da halin da kasar Sin take ciki, to, za su fuskanci babbar matsalar da ta wuce yadda suke zato. Don haka da farko dai masana'antun kasar Sin da suke neman habaka harkokin cinikayyarsu a kasashen Afirka dole ne su yi kokarin gudun karya dokoki. Tilas ne su yi cikakken bincike kan kasuwar kasar tare da kara saninsu kan dokokinta, wannan na da muhimmanci matuka."(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China