in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana daukar nauyin gina wani sabon layin dogo a gabashin Afirka
2014-02-01 15:39:19 cri






Kasar Kenya ta kasance babbar kofa ta gabashin Afirka, kuma ta zama mahadar zirga-zirga a wannan yanki. Amma a halin yanzu kasar tana da layin dogo daya tilo wanda ya taso daga Nairobi, babban birnin kasar zuwa birnin Mombasa da ke bakin teku a gabashin kasar. Wannan layi mai tsawon kimanin kilomita 300 idan ana son binta, to, za a kashe lokaci da ya kai kusan awoyi fiye da goma. Samun koma baya a fannin gina layin dogo ya hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar Kenya, kuma ya kawo cikas ga zaman rayuwar jama'ar kasar. A 'yan shekarun baya, kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar gina hanyoyin jiragen kasa wato layin dogo,abin da ya jawo hankulan jama'ar Kenya, wadanda suke son samun taimako daga kasar Sin. Yanzu ganin yadda kamfanin kasar Sin ya fara gina wani sabon layin dogo a kasar Kenya, yasa jama'ar kasar suke sa ran ganin cimma burinsu nan ba da dadewa ba.

Layin dogon da ya hada Nairobi da Mombasa, an gina ta a karshen karni na 19. Bayan shekaru fiye da dari, har zuwa yanzu ana amfani da wannan hanya wadda ba ta da fadi, kuma har zuwa yanzu ta kasance hanyar jiragen kasa daya tilo a duk fadin kasar Kenya. Sabo da kayayyakin da aka yi amfani da su wajen shimfida layin dogon sun tsufa kwarai kuma an dade ba a kula da shi sosai ba, sakamakon haka saurin tafiyar jiragen kasa a kan layin ya yi kasa da kilomita 40 kan awa daya. Ko da yake nisan dake tsakanin Nairobi da Mombasa kilomita 300 ne kawai, amma idan aka yi amfani da layin jiragen kasa, to, za a kashe lokaci sa yawa kamar sama da awoyi 10. Ban da wannan matsalar ta bata lokaci kuma, a kan samu hadari a kan layin, don haka an kasa tabbatar da lafiyar fasinjoji da kayayyakin da ake jigilar da su ta wannan layin.

A zantawar shi da wakilin gidan rediyon kasar Sin CRI, babban sakataren ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Kenya Mista Nduva Muli ya bayyana cewa, samun koma baya wajen gina layin dogo ya hana bunkasuwar tattalin arzikin Kenya da ma na duk wannan shiyya baki daya. Ya ce,

'Yawan kudin da ake kashewa bisa zirga-zirga a Kenya da duk yankin gabashin Afirka ya kai kashi 40 zuwa 45 bisa dari na darajar kayayyaki da aka kera, amma matsakaicin matsayi a duk duniya kashi 15 bisa dari ne kawai, wannan dai ya sanya kayayyakin da muka kera ba su da karfin takara ko kadan a kasuwannin duniya.'

A halin yanzu dai, zirga-zirgar cikin gida na Kenya da kuma tsakaninta da kasashe makwabta ta dogaro kan hanyoyin mota. Bisa bayanin da Mista Nduva Muli ya ba mu, an ce, yawan kayayyakin da ake jigilar ta jiragen kasa daga Nairobi zuwa Mombasa ya kai ton miliyan 1 da dubu 600 a ko wace shekara, wanda ya kai kashi 5 bisa dari na dukkan kayayyakin da ake jigilar a kasar Kenya. Amma yana ganin cewa, za a canza wannan yanayi a nan gaba ba da dadewa ba. Ya ce,

'Sabon layin dogon da ake ginawa zai canza kasar mu kwarai, haka kuma wannan layi zai zama jagora a fannonin zirga-zirga da jigilar da kayayyaki a kasar Kenya. Wannan layi dai zai rage kudin da ake kashewa wajen yin cinikayya, haka kuma zai sanya kasar mu ta kara bude kofa ga duniya.'

Layin da Mista Nduva Muli yake magana a kai shi ne wani sabon layin dogon da kamfanin Sin ta samu kwangilar aikin gina shi. A ranar 28 ga watan Nuwamba na shekara ta 2013, an kaddamar da aikin a hukumance, inda kamfanin gine-ginen hanyoyi da gadoji na kasar Sin ne ya samu kwangilar aikin shimfida layin, wanda zai kasance wani sabon layin da aka gina shi bisa ma'aunin duniya da ya hada biranen Mombasa da Nairobi. Mataimakin babban manajan reshen kamfanin gine-ginen hanyoyi da gadoji na Sin da ke Kenya Mista Xiong Shiling ya bayyana cewa, bisa shirin da aka yi, an ce, za a fara yin amfani da wannan layin da zai taso daga Mombasa zuwa Nairobi a shekara ta 2018 a hukunce. Zuwa lokacin, za'a dauki awoyi hudu ne kawai daga Mombasa zuwa Nairobi idan aka yi amfani da wannan hanyar, wannan dai zai taimaka sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin wurin. Ya ce,

'Bayan da aka fara yin amfani da wannan layin da muke shimfidawa, za a kara jigilar da kayayyaki, kana kudin da za a kashe wajen jigilar da kaya zai ragu da kashi 60 bisa dari. A wajen lokacin da ake bukata kuma, za a rage shi daga awoyi 15 na yanzu zuwa awoyi 4. Wannan aiki kuma zai samar da guraben aikin yi fiye da dubu 20 ga mazauna wurin, har ila yau wannan zai sa yawan darajar kayayyakin da kasar Kenya ta samu wato GNP ya karu da kashi 1.5 bisa dari.'

Wani kwararre na kasar Kenya Mista Paul Mbugua ya shafe shekaru da dama yana zama a kasar Sin. Ya ce, a lokacin zamansa a kasar Sin, Sin ba ta layin dogo na jiragen kasa masu saurin gaske, amma daga baya sai a kikiron jirgin, an kuma shimfida layin, hakan ya burge shi sosai, don haka da ya koma kasarsa ta Kenya, har kullum yana jiran samun jirgin kasa mai saurin tafiya kamar na kasar Sin. Ya ce,

'Na shafe shekaru da dama ina zama a kasar Sin, idan na fita waje, na kan zabi jiragen kasa. Na tuna da na tashi daga Chengdu zuwa Wuhan, inda na zarce larduna uku, akwai nisa sosai. Amma saurin tafiyar jiragen kasa ya kai kilomita 120 a ko wace awa, don haka lokacin da ake bukata bai kai awoyi 15 ba. Saboda haka ina ganin cewa, ya kamata mu 'yan kasar Kenya mu ma mu yi kokarin samun irin wannan jirgi mai saurin tafiya.'

A ganin shehun malami mai nazarin tattalin arziki da aikin sufuri a Jami'ar Nairobi Mista Kennedy Osoro, abin da Kenya da wannan shiyya suke bukata a cikin shekaru fiye da goma masu zuwa shi ne jirgin kasa mai saurin tafiya. Ya gaya wa wakilin CRI cewa, jirgin kasa mai saurin tafiya da Kenya za ta samu bisa taimakon kasar Sin zai amfanawa ci gaban aikin gona na kasar. Ya ce,

'Muna bukatar wani sabon layin dogo don raya aikin gona, sabo da layin dogo zai iya zuwan wuraren da motoci ba su iya ba, har ma zai yiwu ya tamakawa kokarin kafa sabbin cibiyoyin birane, da samar da kasuwanni ga amfanin gona, da sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya da muke da sauran kasashen duniya.'

A nan gaba ba ma Kenya kawai za ta samu moriya daga wannan sabon layin dogo ba. Bisa shirin da aka yi, layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi zai sa yankin ya zama wani muhimman sashi da ke arewacin gamayyar gabashin Afirka. A nan gaba kuma, za a kara habaka wannan layi zuwa kasar Uganda, a yamma kuma za a habaka shi zuwa Kongo(Kinshasa), haka kuma za a habaka shi zuwa kudu don ta zarce Ruwanda ta yadda za ta kai ga Burundi, za a kuma habaka shi zuwa arewa don ya isa Sudan ta Kudu, ta yadda zai zama wani babban layi mai mihimmanci matuka a nahiyar Afirka. Zuwa lokacin, kasashen da ke dab da wannan layi za su ci moriya sosai.( Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China