140129-Layin-dogo-da-kasar-Sin-ta-taimaka-wajen-shimfidawa-a-kasar-Najeriya-zai-kawo-alheri-ga-jamaar-kasar-Bilkisu
|
A watan Afrilu na shekarar 2006, lokacin da tsohon shugaban kasar Sin a lokacin, wato mista Hu Jintao ya ziyarci tarayyar kasar Najeriya ya tsaida kudurin cewa, gwamnatin kasar Sin ce za ta ba da wasu rancen kudi, tare da wasu kudaden da gwamnatin kasar Najeriya za ta tattara, za a kara inganta ayyukan zamanintar da layoyin dogo na kasar ta Najeriya. Cikin su akwai layin dogo da zai ratsa ta birnin Abuja da birnin Kaduna na jihar Kaduna da katafaren kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CCECC zai taimaka wajen shimfidawa, wanda ya zama daya daga cikin jerin ayyukan. Wannan layin dogon da ya hada babban birnin kasar Najeriya da muhimmin birnin da ke arewacin kasar ba kawai zai kawo alheri ga jama'ar wurin ba, har ma ya samar da dama mai kyau ga wani saurayi na kasar Sin, da wata budurwa 'yar kasar Najeriya fadawa kogin soyayya, daga bisani kuma suka yi aure. Ana iya cewa, wannan layin dogo ya kulla zumuncin auratayya a tsakanin kasashen Sin da Najeriya.
Wannan layin dogo da ya ratsa ta Abuja da Kaduna an soma shimfida shi ne daga shekarar 2011, kuma za a kammala shi a karshen shekarar nan ta 2014. Bayan da aka fara zirga-zirgar jirgin kasa a kan wannan layin dogo, za a kawo karshen tarihin rashin layin dogo tsakanin wadannan muhimman yankunan biyu, haka zalika idan aka bi jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna za'a shafe kimanin awa daya da rabi ne kacal, hakan dai za'a sassauta matsalar cunkoson motoci a kan hanyoyin da suka hada da Abuja, jihar Niger da kuma jihar Kaduna.
Tanko Audu, wani ma'aikacin gwamnati ne dake aiki a birnin Abuja, iyalansa suna zaune a birnin Kaduna. A kowanen karshen mako yana komawa gidan iyalansa, amma bin hanyar komawa gida ta kan kawo masa matsala sosai, saboda haka yana sa ran ganin an fara zirga-zirga a kan layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna.
"Iyalaina suna zaune a Kaduna, ni kuma ina aiki a Abuja, kowace ranar Jumma'a da yamma, ina kama hanyar Kaduna, to ga hanyoyinmu babu kyau ga kuma barayi a hanya, to amma ka ga yadda nake jin labari a yau da na halarci wannan kaddamarwa ta aikin hanyar layin dogo ana cewa, awa daya ya ishe ni daga Kaduna zuwa nan Abuja, to gaskiya ni ina farin ciki kuma zai kara dankon zumuncin da ke tsakanina da iyalaina, ka ga zan kwana a gida da safe sai in fito in zo na yi aiki a nan, idan na tashi in sake shiga layin dogo ya sake komawa da ni Kaduna, ka ga gaskiya na fi kowa ma farin ciki ni karan kaina."
Layin dogo da ya hada Abuja da birnin Kaduna, ba kawai zai taka rawa wajen warware matsalar bin hanya da jama'ar kasar ta Najeriya suke fuskanta ba, a sa'i guda ya samar da yawan guraben ayyukan yi ga jama'ar kasar, kana da ba da horo ga ma'aikatan kasar. Bisa kididdigar da aka samu daga kamfanin CCECC, an ce, kawo yanzu, ayyukan shimfida wannan layin dogo ya samar da guraban ayyukan yi ga mutanen kasar ta Najeriya sama da 4000, kuma bayan da aka fara zirga-zirgar jiragen kasa, za a kara samar da horo da yin hayar ma'aikata 'yan Najeriya sama da dubu 5. Bayan da ya ziyarci yadda ake shimfida layin dogon, 'dan majalisar dattawa na jihar Zamfara, malam Sahabi Ya'u ya nuna matukar yabonsa cewa,
"Wannan aiki ne da ya shafi kimmiya da sauransu, don haka a lokacin da ake saukar da shi wannan layin da ake hakawa, ai yawancin mutanen da ke wurin 'yan Najeriya ne, illa dai akwai wadanda su masana ne a kan kimiya ta haka wannan layi ba da hannu ba, wajibi ne su tsaya su ga cewa, hakika abin yana tafiya kamar yadda ya kamata. Kuma a wannan suna koyawa 'yan Najeriya wannan aikin, suma sun fada da kansu."
A yayin bikin kaddamar da layin dogo, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Mohammad Namadi Sambo ya bayyana cewa, wannan layin dogo da ya hada Abuja da Kaduna ya kasance layin dogo na farko wajen kafa tsarin layukan dogo na zamani a kasar ta Najeriya, hakan dai ya taka muhimmiyar rawa kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
"Yana da muhimmanci, saboda wannan aikin jirgi na tsakanin Kaduna da Abuja, yana daya daga cikin muhimman alkawuran da muka yiwa mutanen Najeriya, kuma yau Alhamdulillahi mun gani karara cewa, wannan alkawari muna cika shi, kuma in sha-Allahu a badi za mu zo nan a wannan tashar jirgin nan mu shiga jirgi daga nan zuwa Kaduna in-sha-Allah."
Aikin shimfida layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna ba kawai zai kawo alheri ga jama'ar kasar ta Najeriya ba, har ma ya hada wani saurayi na kasar Sin da wata budurwa 'yar kasar Najeriya.
Yan Zhiming, mataimakin manaja na sashen kasuwanci dake kula da aikin shimfida layin dogon, wanda ya soma wannan aiki a watan Yuli na shekarar 2008, don gudanar da aikin yin safiyo. Shi ne wani saurayi mai cike da farin ciki, kuma ya iya Turanci sosai. Saboda haka ne, shi da abokan aikinsa suka fahimci juna ba tare da bata lokaci ba, ciki har da wannan budurwa 'yar kasar Najeriya mai suna Juliet Onyingye Agu. Yayin da ta waiwayi lokacin da ta ga Yan Zhiming karo na farko, Juliet ta bayyana kamar haka:
"Ya shiga ofishinmu don daukar wasu takardu, daga baya sai ya fara fassarawa. Mun yi amfani da tebur guda, mun zauna fuska da fuska. Can kuma sai muka fara yin hira, na tambaye shi cewa, ko kana da budurwa? Daga nan ne fa muka soma sanin juna."
Bisa karuwar cudanya da aka yi tsakaninsu, wadannan matasa biyu da suka zo daga kasashe daban daban sun soma yin hira kan zaman rayuwa, ayyuka, kasar Sin, kasar Najeriya, da hakan dai sannu a hankali suka shiga kogin soyayya. Ko da yake sun fuskanci tirjiya daga wajen iyayensu, amma duk da haka sun nemo takardar shaidan aure a shekarar 2010. Yan Zhiming ya ce, shi da Juliet sun tabbatar da cewa sakamakon aikin dogon layi na Abuja da Kaduna, kana saboda dalilin wannan layin dogo ne suka kara fahimtar juna har ma suka shiga kogin soyayya, hakan dai ya sa ya samu wani sabon ra'ayi kan rayuwa:
"A nan gaba, yaranmu za su ce, kamfanin iyayensu ne ya shimfida dogon layin zamani na farko da kasashen Sin da Najeriya suka hada kai don ginawa. Wannan yana da ma'ana a gare mu, shi ne kuma zai kara ma yaranmu kwarin gwiwa sosai. Ta hakan za su san cewa, kamata ya yi su fita waje, don kara zumunci na hada kan al'adu iri daban daban."
Aminu, abokin aikin Yan Zhiming da Juliet ne. Ya gaya mana cewa, auren a tsakaninsu biyu, wata irin haduwa ce a tsakanin mutane biyu da ke da bambancin al'adu da al'umma, lallai sakamakon aikin shimfida layin jirgin kasa na zamani a kasar Najeriya, an hada jama'ar kasashen biyu sosai.
"Wannan aure yana kara dankon dangantaka da karbuwa da kuma kaunar juna, ka san yadda aure ya ke, aure ne na soyayya, tana son shi yana sonta, kuma ga shi ita 'yar Najeriya shi Basine, aure ne da ke nuna cewa, duk daya muke, saboda suna zaman lafiya da soyayya da annashuwa har abin ma abin sha'awa ne yawancin 'yan-uwansa da 'yan uwanta idan suka zo suka ji ko baki idan suka zo, idan aka ce musu ai mijinta ne sai su yi ta mamaki. So abu ne mai kyau, ya kamata a ci gaba da irin wadannan abubuwa a ba da goyon baya a irin wadannan abubuwa saboda yana kawo al'umma su zama daya ya hada kai kuma."
To, masu sauraro shirinmu na yau a cikin shirye-shiryenmu na musamman da muka tsara dangane da huldar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika. Muna fatan kun amfana,a madadin Bilkisu da ta shirya muku shirin, ni Fatimah Jibril dana gabatar ke cewa ku huta lafiya daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin CRI.