in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dabarar kamfanonin kasar Sin wajen neman samun ci gaban harkokinsu a nahiyar Afirka
2014-01-25 16:55:27 cri

A ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2013, an fara yin amfani da wasu sabbin injuna masu samar da wutar lantarki da karfinsu ya kai Megawatt 180 da kamfanin kasar Sin Sinohydro ya sanya ma madatsar ruwa ta Kariba dake kasar Zambia. A wajen bikin kaddamar da sabbin injunan, shugaban kasar Zambia Michael Chilufya Sata ya yaba ma kamfanin Sinohydro kwarai, inda ya ce injunan da kamfanin ya sanya za su sassauta yanayin karancin wutar lantarki a Zambia,da taimakawa samar da karin guraben aiki, gami da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar.

Zancen shugaba Sata gaskiya ne ba romon baka ba, idan an lura da gibin da kasar Zambia ke da shi a fannin wutar lantarki wanda ya kai kimanin Megawatt 350, duk da manyan kogunan da kasar ke da su, wadanda suka kai kashi 40% daga cikin daukacin kogunan dake kudancin nahiyar Afirka. Bisa hasashen da hukumar kasar ta yi, an ce kasar za ta iya samun karuwar tattalin arziki da ta kai kashi 5% a duk wata shekara daga cikin shekaru 10 masu zuwa, amma karuwar wutar lantarki da ta samar ba za ta wuce kashi 3% ba. Hakan ma ya shaida yadda karancin wutar lantarki ke gurgunta kokarin kasar Zambia na neman raya tattalin arziki da bunkasa masana'antu.

Don daidaita wannan matsala ne ya sa aka gudanar da aikin habaka madatsar ruwa ta Kariba wanda kamfanin Sinohydro na kasar Sin ke daukar nauyin shi. Reshen kamfanin dake Zambia ya kwashe kusan shekaru 5 yana kokarin gudanar da aikin tare da haye wahalhalu sosai, a karshe ya kammala aikin wata daya kafin wa'adin ya cika. Dalilin da ya sa kamfanin ya iya kammala aikin yadda ake bukata, a ganin babban darektan kamfanin Liu Benjiang, shi ne kokarin da suka yi domin sanya ayyukansu dacewa da muhallin wurin. Ya ce,

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda muka fahimci yanayin kasuwannin wurin, da ka'idojin kasa da kasa, don haka mun san dabarar da za mu dauka wadda ta dace da yanayin kamfaninmu."

Manufar da Liu ya bayyana tana da sauki, amma yunkurin aiwatar da ita zai shafi ayyuka da yawa, misali: daidaita fasahar sarrafa inji. Kan wannan batu, Liu ya bayyana cewa,

"A madatsar ruwa ta Kariba, ana yin amfani da wasu tsoffin injunan da wasu kasashen yamma suka kera, wadanda suka kunshi fasahohin da suka sha bamban da namu. Amma tun da ana amfani da injunan, tilas ne mu yi kokarin daidaita fasahohinmu ta yadda za su dace da injunan. A wannan fanni mun yi ayyuka da yawa, ga misali, don daidaita fasahar sarrafa inji, sai da muka kwashe shekaru 2 kadai."

A cewar mista Liu Benjiang, don sanya hukumar Zambia ta yarda da ma'aunin kasar Sin a fannin fasaha, da farko an yi kokarin tabbatar da ingancin ma'aunin kasar Sin, sa'an nan an yi bayani kan abun sosai don sanya a fahimci ma'aunin na kasar Sin. Irin kokarin aiki, da mallakar fasahohin ci gaba, da samun ingancin aiki, da sanin bukatun da ake da su, da kokarin bin ka'idoji, sun sa kamfanin Sinohydro ya samu karbuwa sosai a kasar Zambia, har ma ya fara daukar nauyin gina dukkan manyan da matsakaitan madatsar ruwa da gwamnatin kasar Zambia ke son ginawa.

Ban da babban kamfanin mallakar gwamnati irin Sinohydro, wasu kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin su ma sun samu damar habaka harkokinsu a kasashen Afirka. Ga misali, Startimes Tanzaniya, wanda aka kafa a shekarar 2011 bisa hadin gwiwar da kamfanin Startimes na kasar Sin da kamfani mai kula da harkokin rediyo da telabijin na kasar Tanzaniya suka yi, shi ma yana tasowa cikin sauri a kasuwannin kasar Tanzaniya.

Yanzu jama'ar kasar Tanzaniya masu yin amfani da hidimar kamfanin Startimes Tanzaniya sun kai kimanin dubu 600. Sa'an nan a Daressalam, birni mafi girma na kasar, Startimes Tanzaniya ya samu masu yin amfani da hidimarsa dubu 370, adadin da ya kai kusan rabin magidantar birnin. Yadda Startimes ya samu nasarar habaka ayyukansa a Tanzaniya, a ganin babban darektan kamfanin mista Zhou Jun, shi ne domin mai da hankali kan bukatun jama'ar wurin. Ya ce,

"Wasu kamfanonin sun dade suna samar da hidima a wurin, sai dai domin sun dade suna babakere kan kasuwannin can, ya sa suka yi sanyin jiki a fannin sabunta fasahohi, da rashin kulawa da bukatun jama'a. Ba su fahimta cewa kallon telabijin daya ne daga cikin manyan bukatun jama'a daban daban ba. Ganin haka ya sa muka fara samar da wata hidima mai inganci kuma da araha, wadda ta shafi dukkanin sassan kasar. Manufar ta sa muka samu karuwa sosai. Yanzu saurin karuwar magidanta masu yin amfani da hidimarmu ya ninka na kamfanin DSTV kusan sau 30. Ka san, DSTV ya shiga Tanzaniya kusan shekaru 20 da suka wuce, har zuwa yanzu yana da masu yin amfani da hidimarsa dubu 30, amma jama'a masu yin amfani da hidimar Startimes sun kai dubu 600."

Yadda Startimes yake lura da yanayin da jama'a suke ciki, da kokarin daukar fasahar da ta dace da yanayin wurin, sun sa kamfanin ya samu damar raya harkokinsa sosai a nahiyar Afirka. Bayan da kamfanin ya fara da shiga kasuwannin kasar Uganda a shekarar 2007, zuwa yanzu ya riga ya kafa rassansa a kasashe 16 dake nahiyar Afirka, kuma jama'a masu yin amfani da hidimarsa sun kai fiye da miliyan 3, jimillar da ta tabbatar da matsayinsa na wanda ya fi saurin habaka da tasiri a nahiyar Afirka cikin kamfanonin irinsa.

Yadda kamfanin Startimes ya samu nasara a kasuwannin Afirka shi ma ya nuna wani sauyin yanayin da aka samu kan dabarar da kasar Sin ke dauka domin zuba jari a kasashen Afirka. A ganin Madam Wu Fang, wata masaniyar kasar Sin dake mai da hankali kan huldar cinikayya dake tsakanin Sin da Afirka, kasar Sin tana kara nuna muhimmanci kan kokarin taimakawa nahiyar Afirka samun karfin raya kanta, yayin da take zuba jari ga nahiyar a shekarun baya. Madam Wu ta ce,

"A shekarun baya mun canza dabara yayin da muke zuba jari a wasu sassan kasashen Afirka da suka hada da aikin kera kayayyaki, gini, sadarwa, rediyo da telabijin, da dai sauransu. A da mu kan gina wasu ofisoshin gwamnati da fadar shugaban kasa, amma yanzu mun karkata ga gina kayayyakin more rayuwa, ga misali, rijiya, kayan ban ruwa, da kayan tabbatar da tsabtar muhalli, da dai makamantansu. A dayan bangaren kuma, mun fi mai da hankali a kokarin sanya al'ummomin Afirka suka samu karfin raya kansu a halin yanzu."

Matakan da kamfanonin kasar Sin suka dauka don kara karfin al'ummomin Afirka na raya kansu sun hada da kara samar da guraben aikin yi ga jama'ar wurin, da hobasan horar da su. Ga misali, a reshen kamfanin Sinohydro dake Zambia, yawan ma'aikata Sinawa kan 'yan Zambia shi ne 1 bisa 6. Kana a nasa bangaren, Startimes Tanzaniya ya mai da horar da ma'aikatan kasar daya daga cikin manyan ayyukansa.

Wadannan matakan da aka dauka sun ba jama'ar wurin damar koyon wasu fasahohi masu ci gaba, gami da rage kudin da kamfanonin suke kashewa, don haka sun amfanawa dukkan bangarorin 2, ma'aikata da kamfani. Sai dai sakamakon bambancin da ake da shi a fannonin al'adu da dokoki, ya sa wasu kamfanonin kasar Sin suka fuskanci wahalhalu a kokarin kula da dangantakarsu da ma'aikatan wurin. Game da batun, shugaban kamfanin Sinohydro Zambia mista Liu Benjiang ya bayyana fasaharsa da cewa,

"Mu kan yi binciken dokokin wurin game da daukar ma'aikata, kana mu kan tattauna dokokin da hukumomi don samun cikakken bayani daga wajensu. Ta haka, mun sanya hukumomi suka halarci aikinmu na kulla yarjejeniya da ma'aikata. Idan daga baya mun ga ba mu fahimci dokokin sosai ba, to, za mu gyara. Idan ma'aikata ba su sauke nauyin dake kansu ba, ita hukuma za ta yi musu bayani."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China