in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya wuri mai kayatarwa ne wajen yawon shakatawa
2014-01-31 15:51:04 cri

Mutane da dama sun san cewa, shahararren marubucin nan Mr Ernest Miller Hemingway ya taba rubuta wani labari dangane da tsaunin Kilimanjaro, wanda ya kasance tsauni mafi tsayi a nahiyar Afrika da ya jawo hankalin mutanen kasashen duniya. Ban da haka, kasar Tanzaniya wadda wannan tsauni ke cikin ta na da shimfidar wuri mai kayatarwa dake jawon hankalin masu yawon shakatawa daga ko'ina a fadin duniya. Tun daga shekarar 2004, kasar Sin ta fara mai da Tanzaniya daya daga cikin wuraren da jama'ar Sin ke yawan yawon shakatawa a wajen, cikin shekaru goma da suka gabata, yawan Sinawa da suka kai ziyara a kasar ya karu sosai, abin da ya samar da zarafi mai kyau wajen yin ciniki.

"Zanzibar garin dake da fadin fiye da murabba'in kilomita 1700, da yawan al'umma kimanin dubu 600. Ganin cewa ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali,don haka akwai karanci aikata laifufuka. Zafin yanayin ya kan kai digiri 38 zuwa digiri 28. Akwai abubuwa tarihi da dama a wannan wuri, alal misali, garin duwatsu, da farko, muna iya ganin coci, kasuwar kayan lambu, sannan akwai kayayyakin tarihi na gargajiya na kasar…"

Karkashin haske rana, Malam Salim Ali mai shekaru 37 a duniya na yiwa masu yawon shakatawa bayani kan tsibirin Zanzibar na kasar Tanzaniya da harshen Sinanci.

Wannan tsibiri tamkar wani lu'u lu'u ne a kan tekun Indian. Ana iya jin dadin zama a kan gabar teku yayin da iska mai sanyi ke bugawa, kuma ana iya ganin yadda al'adun nahiyar Afrika ya hadu da al'adun Larabawa da Indiya ta hanyar yawon bude ido a garin duwatsu, sannan kuma ana iya yin wasa da kifin Dolphins cikin teku, har ma a yi iyo tare da kifaye a cikin teku. Ko wace shekara, Zanzibar na karbar baki masu yawon shakatawa daga wurare daban-daban a duniya, daga cikinsu akwai Sinawa da dama. Ganin haka ya sa Salim Ali ya zama wani mai ba da jagoranci ga masu yawon shakatawa musamman ma Sinawa.

Bayan shekaru biyu da ya koyi Sinanci a wurin, sai Ali ya tafi lardin Henan na kasar Sin, inda ya kwashe watanni shida yana koyon Sinanci da fasahar motsa jiki da fadace-fadace ta gargajiyar kasar Sin wato Kong Fu. Daga baya ya koma gidansa dake Zanzibar a shekarar 2012, inda ya kafa wata makarantar bada horo kan fasahar Kung Fu. Daga baya ya fahimci cewa, akwai Sinawa da dama da suke zuwa Zanzibar domin yawon shakawata,don haka sai ya fara aikin ba da jagoranci ga masu yawon shakatawa da Sinanci. Ya ce

"Tun lokacin da na dawo nan daga kasar Sin a shekarar 2012, na fara wannan aiki daga watan Fabrairu, har zuwa yanzu, na karbi Sinawa 85, wannan adadi zai karu saboda ganin yawan Sinawa da su kan zo yawon shakatawa zai karu nan gaba. Da farko na fara da karbar bakuncin mutum daya zuwa biyu a karo daya, amma yanzu, na kan karbi babbar kungiyar dake kunshe da mutane fiye da 60."

Ba ma kawai masu yawan yawon shakatawa da suka ziyarci Zanzibar ya karu ba, har ma Tanzaniya ta zama wuri da ya fi jawon hankalin masu yawon shakatawa Sinawa tun daga shekarar 2004. Wani babban jami'in hukumar yawon shakatawa ta kasar Tanzaniya Aloyce Nzuki ya nuna cewa, yanzu yawan Sinawa da suke ziyara a kasar yana karu da kashi 3 bisa dari a ko wace shekara, musamman ma bayan ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai a Tanzaniya a watan Maris na shekarar 2013. Ya ce

"Mr Xi Jinping ya tabo wurare masu ni'ima da dama cikin jawabin da ya yi a lokacin da yake ziyara a Tanzaniya, ciki hadda lambun shan iska na Serengeti na kasar, tsaunin Kilimanjaro da tsibirin Zanzibar, matakin da ya sa Sinawa fiye da dubu daya suka fara zura ido kan wurare masu kayatarwa na kasar, kuma ya taimaka wajen janyon hankalin Sinawa masu yawon shakatawa zuwa nan Tanzaniya."

Tanzaniya ta samu yabo sosai kan shimfidar wurinta masu kayatarwa, ban da tsiribn Zanzibar, tabkuna uku mafi girma a nahiyar Afrika wato tabkin Victoria, tabkin Tanganyika da tabkin Malawi suna kan layin iyakar kasar. Ban da haka, tsaunin mafi tsayi a nahiyar Afrika,wato Kilimanjaro yana zaune ne a kasar wanda ya yi shahara sosai. Sa'an nan wani babban dalilin da ya sa aka kasa magance wannan kasa yayin da ake tsara shirin yawon shakatawa shi ne albarkatun dabbobi da kasar ke da su. Yanzu kasar ta mallaki manyan lambunan shan iska 16 da yankunan kiyaye dabbobi da ni'imtattun wurare 23, fadinsu ya kai kashi 28 bisa dari na dukkan fadin kasar, abubuwa da suke jawo hankulan mutanen kasashen duniya sosai.

Pius Madale mai shekaru 60 a duniya wani gwani ne wajen ba da jagoranci ga masu yawon shakawata, yana da fasaha sosai wajen ba da jagoranci a yankunan dake da namun daji. Ya bayyana ma manema labarai cewa, ko da yake, yawan Sinawa bai kai na mutane daga kasashen yammaci ba, amma yawansu ya karu tun daga shekarar 2008, musamman ma a shekaru uku da suka gabata, yawan Sinawan da ya karba ya kai fiye da 200. A ganinsa, Sinawa na mutumta al'adun wurin, kuma na ba da gudunmawa sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin wurin, abin da ya sa, mazauna wurin ke maraba da Sinawa sosai. Ya ce

"Sinawa na mutunta al'adunmu, kuma suna kaunar dabbobi sosai, ban da haka, suna son sayen abubuwa. Abin da ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arizki a wasu wurare. Ka san masu sayar da kananan abubuwa da yawa ba su da kudi sosai, saboda haka, suna Allah-Allahr ganin zuwa Sinawa masu yawon shakatawa wadanda za su taimaka musu sosai a fannin samun kudin shiga."

Albarkatun yawon shakatawa mai kyau na Tanzaniya ba ma kawai yana jawo hankalin masu yawon shakatawa Sinawa ba, har ma ya jawo hankalin masu zuba jari. Zheng Ying wata budurwa ce 'yar asalin lardin Guangdong ta kasar Sin mai shekaru 26 a duniya, wadda ta kwashe shekaru 3 tana aiki ba da jagora a kasar Tanzaniya. Dalilin da ya sa ta yanke shawarar samun aiki a Tanzaniya shi ne ziyarar da ta yi a nahiyar Afrika a shekarar 2011. Ta ce

"Jama'ar wurin kuma wasu abokaina Sinawa sun gaya mini cewa, Tanzaniya na da albarkatun yawon shakatawa sosai, don haka akwai makoma mai haske idan na yi aiki a wannan fanni. Shi ya sa, na sami izni daga iyayena, na kuma himmatu wajen bude wani kamfanin yawon shakatawa da abokaina mai suna 'tunanin Afirka', wanda yake baiwa Sinawa hidima domin su yi yawon shakatawa a kasar Tazaniya cikin sauki."

Kudin da Zheng Ying ta samu bisa kula da wannan kamfanin ya mayar da wanda ta kashe a shekara ta farko, domin karuwar yawan Sinawa da suke kai ziyara a Tanzaniya ta sa kamfanin ya samu baki sosai. Ya zuwa yanzu, Zheng ta dauki ma'aikata 6, wadanda suka karbi kungiyoyi daga kasar Sin fiye da 10, hakan ya sa, kamfaninta ya shiga sahun gaba wajen yawan karbar baki 'yan yawon bude ido tsakanin kamfanonin da Sinawa suka kafa. Game da sha'anin yawon shakatawa a Tanzaniya, Zheng Ying na da kwarin gwiwa sosai, ta ce

"A ganina, Tanzaniya na da makoma mai haske sosai a wannan fanni a cikin shekaru 20 masu zuwa, ban da haka, akwai wuraren yawon shakatawa masu kyau a wurin. Ya zuwa yanzu, Sinawa da dama na fatan yawon bude ido a kasashen waje, saboda haka, ina sa ran ganin karuwar Sinawa 'yan yawon bude ido a kasar Tanzaniya."

Ban da Zheng Ying, idan ba a manta ba, Salim Ali dan kasar Tanzaniya wanda yake kaunar taliyar lardin Henan da fasahar Kung Fu sosai ya yi shiri tsaf kan aikinsa. Ya ce.

"Ina fatan habaka aikina na sha'anin yawon shakatawa. Zan yi kokari in ba da hidima ga Sinawa. Nan gaba kashi 90% na bakin da zan karba Sinawa ne." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China