130207-aladar-sinawa-ta-kirga-shekaru-da-dabbobi-lubabatu
|
Tun tuni a karni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihisalam, Sinawa sun fara yin amfani da dabbobi 12 wajen kirga shekaru, kuma ya zuwa karni na 5 zuwa na 6, al'adar ta riga ta zama ruwan dare. Bayan kirga shekaru, kakan kakanin Sinawa sun kuma yi amfani da dabbobin 12 wajen kirga watanni da kuma lokuta na kowace rana.
Game da me ya sa kakanin kakanin Sinawa suka fara kirga shekaru da sunayen dabbobi, dalili shi ne sabo da ilmin da suka samu game da taurari. A zamanin da, kakanin kakanin Sinawa sun gano cewa, lokacin zafi da lokacin hunturu suna canzawa, kuma wata ya kan cika har sau 12 cikin shekara guda, sabo da haka, sun tsai da dabbobi 12 wajen kirga shekaru. Kuma sun sanya su cikin wani jeri, inda suka jera bera, saniya, damisa da sauran dabbobi a ciki.