130131-bikin-chunjie-a-kasar-sin-lubabatu
|
Wasu al'adun da suka shafi bikin:
Jajiberen bikin bazara yana da muhimmanci sosai ga Sinawa. A jajiberen, Sinawa su kan hadu da iyalansu gaba daya, suna cin abinci suna hira a duk dare, abin da Sinawa ke kira Shousui ke nan.
Bayan jajiberen, a rana ta farko cikin sabuwar shekara, Sinawa su kan sanya sabbin kaya masu kyau, su je gaida dangogi da abokai, don nuna musu fatan alheri, abin da muke kira Bainian ke nan da Sinanci. Bayan haka, akwai kuma wata muhimmiyar al'adar da Sinawa kan bi a lokacin da suka mika gaishe-gaishe ko kuma karbar gaishe-gaishe na sabuwar shekara. Wato idan yara suka mika gaishe-gaishe na sabuwar shekara ga tsofaffi, wato tsofaffi su kan ba da kyautar kudi cikin wata karamar jar jaka a gare su, kudin da Sinawa ke kira Yasuiqian ke nan, domin bayyana fatan alheri ga yara da su girma cikin lafiya a sabuwar shekara.
A lokacin bazara, Sinawa su kan manna sakwanni na taya murnar sabuwar shekara da nuna fatan alheri a gefunan kofar gidansu, wadanda aka rubuta a kan takardu masu launin ja, domin bayyana burinsu na samun alheri cikin sabuwar shekara. A kan kofa kuma, akasari a kan manna wata babbar kalmar Sinanci da aka rubuta a kan wata jar takarda, kalmar da ta kasance alheri idan muka fassara.
A wasu sassa, musamman karkara, a kan kuma manna zane-zane a kan kofa, zane-zanen da suka shafi samun albarka da alheri cikin sabuwar shekara.
Sinawa suna da al'adar yin wasan wuta a lokacin bikin bazara. Game da dalilin wannan al'ada, akwai wata tatsuniya. Sinawa suna kira bikin bazara kamar Nian, kuma bisa tatsuniyar gargajiya, Nian ya kasance dodon da zai iya kawo sharri, wanda idan ya zo, sai bishiyoyin su bushe, da ya tafi kuma, sai su farfado. Dodo ba ya tsoron kome ban da wuta da haske. To, don korarsa, Sinawa su kan yi wasan wuta a lokacin bikin bazara. Amma yanzu haka, Sinawa suna yin wasan wuta ne domin murnar shiga sabuwar shekara tare da nuna fatan alheri. Sinawa suna da wani tarihi na tsawon shekaru dubu biyu na yin wasan wuta, kuma su kan yi wasan wuta musamman a lokacin da ake samu wani abin da ake murna a kai, ko bukukuwa ne, ko aure ne, duk a kan yi wasan wuta, domin nuna murna da fatan alheri.
A lokacin bikin bazara, Sinawa a sassa daban daban su kan kuma shirya shagulgula iri iri, inda su kan nuna wasanni iri iri masu ban sha'awa, domin nishadantarwa. A zamanin yanzu, Sinawa suna kuma son yawon shakatawa a lokacin bikin bazara.
Sinawa su kan shafe tsawon kwanaki 15 suna bikin bazara, kuma a rana ta 15, a kan shirya bikin Yuanxiao, ko kuma bikin fitila, bikin da ya kawo karshen bikin bazara ke nan. A ranar, da dare ya yi, a kan daga fitilu iri iri masu ban sha'awa, kuma jama'a su kan fita waje suna kallon fitilu suna murna.