in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mu'amalar al'adu ya kusantar da jama'ar Tanzania da kasar Sin
2014-01-24 19:48:50 cri

Yau shekaru gwammai da suka gabata, a duk lokacin da aka ambaci kasar Sin, abin da akasarin mutanen kasar Tanzania su kan tuna shi ne hanyar dogo da ta ratsa Tanzania da Zambia da kasar Sin ta gina. To, amma idan aka ambaci kasar ta Sin a zamanin yau da muke ciki, abin da mutanen Tanzania su kan tuna shi ne wani wasan kwaikwayon talabijin mai taken Doudou da surukarta, wasan da aka juya shi zuwa harshen Kiswahili ba kawai ya samu matukar karbuwa daga al'ummar kasar ba, hatta ma ya sa sun fara sha'awar koyon Sinanci.

"Sunana Shabani, ni mutumin Tanzania ne, kuma ina da shekaru 26 da haihuwa. Ina son koyon Sinanci,kuma ina son zuwa kasar Sin koyon Sinanci. A halin yanzu, mutanen Zanzibar na son koyon Sinanci." Shabani Juma Rashid Mnyuke dalibi ne a kwalejin koyon ilmin labarai na Zanzibar. Bayan da ya shafe tsawon shekaru biyu yana koyon harshen Sinanci a cibiyar Confucius da aka kafa a kwalejin, yau ga shi ya iya magana da Sinanci.

Dalibai irinsu Shabani da ke iya magana da Sinanci suna da yawa a wannan kwalejin. Tun bayan da aka kafa cibiyar Confucius a kwalejin a shekarar 2009, cibiyar ta koyar da Sinanci ga dalibai sama da 300. Kiswahili da Turanci harsuna ne da ake amfani da su a wurin, amma yanzu Sinanci ya zamanto wani harshen waje da dalibai a kwalejin suka fi sha'awar koyo.

A game da me ya sa suke son koyon Sinanci, daliban sun ba mu dalilai daban daban."Sabo da Sinanci na da dadin ji, ina son Sinanci sosai. Ban da haka, lafazin Sinanci ya yi kama da na Kiswahili, shi ya sa ina ganin yana da saukin koyo gare ni, dalili ke nan da ya sa nake son koyo." "Dalilina shi ne ina fatan harshen zai taimake ni wajen samun aikin yi. Ko bayan da na yi ritaya ma, ina son yin amfani da Sinanci. Saboda kasar Sin kasa ce mai wadata, wadda take saurin bunkasa."

Wadannan dalibai ba kawai suna koyon Sinanci ba, har ma suna koya ma saura Sinanci. Wani dalibi mai suna Omar Kombo Rashid ya ce, "Ina son koyon Sinanci sosai, babu wuya gare ni. Amma ba zan tsaya a nan ba, bayan da na kammala karatu, zan ci gaba da kokari, sabo da ina son Sinanci kwarai. A lokacin da nake tare da iyalaina, ina son yarana ma su koya. Wani lokaci idan ina kan titi, na kan koya wa wasu yara Sinanci kadan kadan, misali yadda ake kirga da Sinanci, yanzu ma sun iya."

A yayin da koyon harshen Sinanci ke kara samun karbuwa a Tanzania, cibiyar Confucius da ke Zanzibar bai iya biyan bukatun al'ummar wurin ba, don haka makarantun firamare da midil da sassan gwamnati da na kasuwanci da dama suka bukaci cibiyar da ta kara habaka wuraren da za ta samar da darrusan koyar da Sinanci.

To, amma me ya sa mutanen Tanzania suke sha'awar koyon Sinanci? Domin amsa tambayar, dole sai mu ambaci wani wasan kwaikwayon talabijin na kasar Sin da aka juya shi zuwa harshen Kiswahili.

A shekarar 2011, wani wasan kwaikwayon talabijin na kasar Sin mai taken Doudou da surukarta da aka gabatar a kasashen gabashin Afirka ya samu matukar karbuwa, wanda har yanzu yake da farin jini. Bisa kididdigar da kamfanin Star Times da ke samar da shirye-shiryen talabijin a Tanzania ya yi, a yayin da ake gabatar da wasan, wasan ya kai ga matsayi na farko wajen samun masu kallo kwatankwacin sauran shirye-shiryen da aka gabatar a wancan lokaci.

Bayan Doudou da surukarta, a watan Nuwamba na shekara ta 2013 kuma, an fara gabatar da sauran wasu wasannin kwaikwayon talabijin guda uku da aka juya su zuwa Kiswahili, wadanda su ma suka samu karbuwa matuka. Omar Ahmed Khamis, wanda ya yi aikin sanya murya ga wadannan wasanni uku ya ce,"wasannin kwaikwayon talabijin na waje da aka gabatar mana a da ba a juya harsunansu ba, don haka ina ganin ba wasanni ne da aka shirye domin mu ba. Amma ga shi yanzu mun juya wasannin kwaikwayon kasar Sin zuwa harshen Kiswahili, 'yan wasan suna magana da harshenmu, abin da ya kawo su kusa da mu."

Sakamakon wasannin kwaiwayon talabijin na kasar Sin, mutanen kasar Tanzania da yawa suka fara sha'awar koyon Sinanci. A ganin Liu Dong, karamin jakadan kasar Sin da ke kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin kasar Sin a Tanzania, hakan ya bayyana sha'awar da al'ummar kasar ta Tanzania suka nuna game da kasar Sin a wannan zamani. Ya ce, "Yadda kasar Sin take bude kofarta da yin gyare-gyare abu ne mai ban mamaki gare su. Sun san cewa, kasar Sin a yau shekaru 30 da suka wuce kusan ba wani bambanci da yadda kasarsu take a yanzu, amma su wadanda suka taba zuwa kasar Sin su kan yi mamaki da halin da kasar Sin ke ciki yanzu bayan ta bude kofarta da yin gyare-gyare. Bisa wasannin kwaikwayon da muka gabatar, suna iya samun masaniya a kan abubuwan da Sinawa ke tunani a kai da kuma yadda Sinawa ke tuntubar juna. Abubuwan da muka nuna sun shafi fannoni daban daban na zaman rayuwa, wadanda suke da sha'awar fahimta. Don haka ne, suna son wasannin kwaikwayon talabijin na kasar Sin."

Shabani Juma wanda a yanzu haka yake kokarin koyon Sinanci ya ce, yana fatan wata rana zai zama wani malamin koyar da Sinanci, domin fahimtar da karin al'ummar kasar kan kasar Sin, ya ce, "Wata rana zan zama wani malamin koyar da Sinanci, sabo da ina fatan harshen Sinanci zai yadu zuwa kowane bangare na Zanzibar da Tanzaniya. Harshen Sinanci yana wakiltar al'adun kasar Sin, haka kuma ya bayyana hadin gwiwar aminci da ke tsakaninmu da aminanmu Sinawa. Yanzu haka mutanenmu da dama suna iya Kiswahili ne kawai, ni zan yi kokarin taimaka musu domin koyar da su, ciki har da mutanen Tanzania da Kenya da Uganda da ma na sauran sassan Afirka. Har ma ina so koya wa Amurkawa Sinanci, abu ne mai ban sha'awa." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China