140124-Sinawa-suna-fi-son-zaben-tafiye-tafiye-danladi
|
A 'yan kwanakin baya, wani shahararren shafin internet na kula da harkokin yawo mai suna Xiecheng na kasar Sin ya bayar da wani rahoto kan binciken da ya yi kan masu yawon shakatawa a shekara ta 2014, inda aka bayyana cewa, Sinawa sun fi shawar ziyartar wurare da kansu yayin da suke yawon shakatawa, kashi 81 bisa dari na masu yawon shakatawa suna bukatar yin haka da kansu. Yawancin ma'aikatan da ke kula da harkokin yawon shakatawa suna ganin cewa, a nan gaba tafiye-tafiye zai zama wata muhimmiyar hanya da ake bi wajen yawon shakatawa, wato Sinawa na zaben wuraren da suke kai ziyara, sa'an nan su sayi tikiti hanyar internet da kansu, kuma su nema shiga cikin tawagogin masu yawon shakatawa bisa burinsu.
Rahoton ya bayyana cewa darektocin kamfanonin yawon shakatawa da yawa sun yi hasashen cewa, a shekara ta 2014, muhimman wuraren da masu yawon bude ido suka zaba su ne, biranen Sanya, da Xiamen, da Qingdao dake dab da tekuna; da Chengdu, da Lijiang da dai sauran biranen samun nishadi sosai.
Ban da wuraren kasar Sin kuma, masu yawon bude ido na zuwa sauran kasashen duniya domin yawon shakatawa, kuma sun fi zaben tsibiran tekunan Pacific, da India, yankunan dake kudu maso gabashin Asiya, wadanda suke kasancewa wuraren gargajiya da Sinawa suka zuwa, ban da wannan kuma suna zaben wuraren da ke makwabtaka da babban yankin kasar Sin, wato wuraren da suka hada da Hongkang, da Macau, da Taiwan, da Korea ta Kudu da dai sauransu.(Danladi)