in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan cibiyar ba da misali kan fasahar noma ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique
2014-01-23 12:32:16 cri

A kasar Sin, akwai wata karin magana dake cewa, hatsi ya fi muhimmanci, ko ga wata kasa, ko ga jama'a, dalilin da ya sa aka fadi hakan shi ne domin hatsi tushe ne na kome da kome. Amma, a kasar Mozambique da ke nahiyar Afirka, ko da yake kasar tana da kasa mai kyau wajen shuke-shuke, duk da haka, ta dade tana shigo da hatsi daga kasashen waje.

Domin taimaka wa jama'ar kasar samun isasshen abincin gina jiki, gwamnatin kasar Sin ta kafa cibiyar ba da misali kan fasahar aikin gona a kasar, ba ma kawai kwararrun da suka zo daga kasar Sin suna koyar da mazaunan kasar yadda suke shuka hatsi a wannan cibiyar ba, har ma suna taimakon kasar wajen bunkasa aikin noma na zamani. A cikin shirinmu na yau, bari mu karanto muku wani bayanin da wakilanmu suka aiko mana.

Wakar da kuka saurara waka ce da matan kasar Mozambique ke rerawa lokacin da suke shuka a gonaki na wannan cibiyar ba da misali kan fasahar aikin gona ta hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Mozambique da ke karkarar Maputo, babban birnin kasar.

Wannan cibiyar ba da misali kan fasahar aikin gona ita ce irin cibiyar ta farko da kasar Sin ta kafa a nahiyar Afirka. Makasudin kafuwarta shi ne domin daga matsayin shuka hatsi a kasashen Afirka, tare kuma da kyautata halin karancin abincin da suke ciki.

A shekarar 2006, an yi taron koli na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda a karo na farko aka yi shawarar kafa wannan cibiyar ba da misali kan fasahar aikin gona ta hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka. A shekarar 2007, a hukumance aka fara gina cibiyar, kuma a shekara 2011, aka mika cibiyar ga gwamnatin kasar Mozambique domin ta fara aiki yadda ya kamata. A sa'i daya kuma, bi da bi ne sauran cibiyoyin ba da misali kan fasahar aikin noma guda 19 da kasar Sin ta yi alkawarin ginawa sun fara aiki daya bayan daya a kasashen Afirka.

A cikin wurin aiki na cibiyar dake karkarar birnin Maputo, gonaki masu inganci sun fi jawo hankalin jama'a, game da hakan, direktan cibiyar Liu Housheng wanda ke rike aikin gona cikin shekaru sama da ashirin da suka gabata shi ma ya nuna gamsuwarsa. Ya ce, "Gonaki a nan na da inganci kwarai, ana iya cewa, sun fi dace da shuka hatsi, kuma cikin sauki ana iya samun girbi mai armashi idan aka zabi irin da suka dace tare kuma da shuka su ta hanyar kimiyya."

A wannan kasar, ba ma kawai gonaki na da inganci ba, har ma yawancin gonakin kasar da fadinsu ya kai hekta miliyan 36 a sararin kasa suke, ban da haka, ruwan sama da hasken rana su ma sun yi yawa a wuraren. A halin da ake ciki yanzu, jama'ar kasar Mozambique kashi 80 cikin dari suna dogaro kan aikin gona. Direkta Liu Housheng ya gaya mana cewa, hadaddun sharudan halittun da suka hada yawan mutane da gonaki masu inganci da yanayi mai dacewa a kasar sun fi na kasar Sin a zahiri.

Duk da haka, wannan kasa da ta dace da bunkasuwar aikin noma tana shigo da hatsi kusan tan dubu dari biyu daga kasashen waje a ko wace shekara, dalilin da ya sa haka shi ne domin wannan kasar dake kudancin Afirka tana fama da karancin hatsi na tsawon lokaci saboda fasahar aikin gona ta gargajiya da ba ta samu bunkasawa yadda ya kamata ba a kasar. Shi ya sa, babban aikin cibiyar ba da misali kan fasahar aikin gona ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique shi ne taimaka wa kasar wajen yin nazari kan fasahar noma, tare kuma da ba da misali da yada fasahar a duk fadin kasar gaba daya, a sa'i daya kuma, a horar da masu aikin fasahar noma, ta yadda za a kawar da matsalar karancin abinci a kasar.

A wurin, 'yan fasahar aikin gona suna iya kara samun yawan hatsin da suka shuka ta hanyar kimiyya da ire-iren da aka samar da su na wurin. Game da wannan, direktan cibiyar Liu Housheng ya ce, "Alal misali, kamar gero, muna shuka su da iri na kasar Mozambique da ake kiransa 'Shangrila', amma, idan an shuka bisa al'adar Mozambique, to, ana iyar samun gero tan 1.5 kawai daga gona hekta daya, idan an yi amfani da fasaharmu, to, za a iyar samun tan 4.5 ne, ana iya cewa, yawan geron da muka samu a gona hekta daya da ke cibiyarmu ya karu da ninki uku idan aka kwatanta da wanda mazaunan wurin suka shuka bisa al'adarsu."

Da zarar mazaunan wurin suka ji labari game da kafuwar wannan cibiyar ta kasar Sin, musamman ma bayan da suka gan karuwar hatsin da aka samu, jama'ar kasar Mozambique da yawan gaske sun zo wurin domin kara sanin fasahar da abin ya shafa, an yi mana bayani cewa, yawancinsu sun zo wurin ne domin su tambayi kwararrun fasahar aikin gona da suka zo daga kasar Sin tambayoyin da suka shafi ire-iren hatsi, da fasahar aikin gona mai saukin koyo, da kananan injunan aikin gona da suka fi dacewa da aikinsu, da kuma yanayi da dabarar shuka hatsi da sauransu.

Manuel dalibi ne wanda ke neman digiri na farko a kwalejin koyon ilmin fasahar aikin gona ta jami'ar Eduardo Mondlane ta kasar Mozambique. Yanzu, yana yin nazari kan batun game da halin da ake ciki yayin da ake kokarin yada fasahar zamani ta cibiyar ba misali ta aikin gona ta kasar Sin. Domin kara samun bayanan da abin ya shafa, Manuel ya kan zo cibiyar, a ganinsa, aikin da cibiyar ke gudanarwa yana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar aikin gonan kasarsa ta Mozambique. Ya ce, kasarsu tana bukatar irin wannan fasahar zamani ta aikin gona kwarai, kuma a tsamaninsa, irin wannan hanyar hadin gwiwa tana da kyau sosai saboda ana iya koyon ilmomi masu amfani da yawa a wurin, musamman ma ga wasu wuraren da ba su samu bunkasuwar tattalin arziki ba tukuna, saboda mutane a wuraren suna dogaro ne kan aikin gona, don haka, sun zo wurin koyon fasahar noma ta zamani, daga baya za su yi amfani da fasahar wajen aikinsu a gonaki, da haka, za su iya samun isasshen abincin da suke bukata, sa'an nan kuma za su iya kubutar da kansu daga talauci, kamar yadda aka sani, karancin abinci babbar matsala ce da yawancin jama'ar kasarsa ke fuskantar.

Bisa rahoton da majalisar dinkin duniya ta bayar, an ce, Mozambique na daya daga cikin kasashen da suke kama baya a duniya, gwamnatin kasar na iya samar da kudi kalilan ne kawai ga jama'ar kasar. Kan wannan, karamin jakadan kasar Sin dake Mozambique Wang Lipei yana ganin cewa, ba ma kawai cibiyar tana ba da misali wajen taimakawa jama'ar kasar sarrafa fasahar noma ta zamani ba, har ma za ta taimake su wajen mai da aikin gona a kasarsu zuwa na zamani. Ya ce, cibiyar ba da misalign a kan aikin gona tana da manyan ayyuka guda biyu, na farko shi ne a nuna wa jama'ar Mozambique fasahar noma ta zamani da tunanin raya aikin noma, tare da horar da 'yan fasahar noma da jami'an aikin noma a kasar, domin kara fahimtarsu kan bambanci tsakanin aikin noma na gargajiya da na zamani. Na biyu kuma, ba da shawara ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Mozambique domin raya aikin gona a kasar.

Ko da yake cibiyar ba da misali kan fasahar noma ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique ta fara aiki ne daga shekarar 2011, wato kawo yanzu, shekaru biyu ne kawai, duk da haka, babban tasirin da ta kawo wa aikin noma na Mozambique ya riga ya jawo hankalin wasu kasashe da kuma kungiyoyin kasa da kasa da dama. Direktan cibiyar Liu Housheng ya yi mana bayani cewa, yanzu, wasu kamfanonin kasashe kamar su Japan da Afirka ta Kudu da wasu kungiyoyi na kasashen Afirka sun ziyarci cibiyar bi da bi domin yin rangadin aiki. Ban da haka, wasu asusun da ke kokarin raya Afirka su ma suna yin hadin gwiwa da cibiyar. Liu Housheng ya ce, "Asusun Bill Gates kan aikin noman shinkafa mai inganci ba tare da gurbata muhalli ba a nahiyar Afirka ya kafa wata tashar jarrabawa a cibiyarmu, yawan ire-iren shinkafar da suka shuka a nan ya kai 30, a watan Fabrairun kuwa, kwararrun aikin za su zo cibiyarmu domin zaben ire-iren da muka shuka, ta yadda za su kara inganta aikinsu."

A kasar Sin, akwai wata karin magana, Sinawa su kan ce, "A koyar wa mutum fasahar kamun kifi ya fi a ba shi kifi a hannu." Direkta Liu Housheng wanda ya yi shekaru da dama yana aiki a Mozambique ya nuna cewa, muddin dai a koyar wa jama'ar kasashen Afirka fasahar noma ta zamani, to za a iya warware matsalar karancin abinci a nahiyar daga duk fannoni.

Pedro wanda ya yi watanni da dama yana karatu a cibiyar ya bayyana cewa, ya koyi abubuwa masu amfani da yawa a wurin, ya hakikance cewa, zai kara kyautata aikinsa na gona nan gaba, ya ce, kafin ya zo wurin, bai iya kome ba, amma yanzu ya iya abubuwa da yawa, musamman ma fasahohin da ake amfani da su yayin da ake gudanar da aiki a gona, Ko da yake yanzu ba shi da gona, amma wata rana idan ya sayi gonaki, to, zai shuka hatsi da fasahar da ya koyi a nan, ko shakka babu, zai cimma burinsa na yin aiki mai kyau. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China