in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hasashen masana game da ci gaban tattalin arzikin Najeriya
2014-01-31 15:52:31 cri

A shekara ta 2001 ne aka fara ambaton kasashen BRICS, wato Brazil, Rasha, Indiya da kuma Sin, kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa.

Wani masanin tattalin arziki mai suna Jim O'neil ne ya yi wannan hasashe, inda yanzu kuma ya ce, rukunin kasashen da ya kira"MINT" wato Mexico, Indonesia, Najeriya da kuma Turkiya sun kama hanyar zama a kan gaba wajen habakar tattalin arziki.

Bayanin masanin game da kasar Najeriya, ya janyo hankalin nahiyar baki daya, kasancewarta ja gaba a nahiyar a dukkan fannoni.

Sai dai, masana na ganin cewa, idan har Najeriya tana son ganin wannan mafarki ya tabbata, wajibi ne ta magance wasu manyan kalubale, kamar matsalar tsaro, wutar lantarki, sufuri, cin hanci da rashawa da dai sauransu, ta yadda za a kara janyo hankulan masu sha'awar zuba jari a kasar.

Bugu da kari, masharhanta na cewa, dangantakar Sin da Afirka, wata babbar dama ce da za ta kara taimakawa kasar ta Najeriya kan hasashen da wannan masani ya yi game da habakar tattalin arzikinta.

Sannan wajibi ne ga 'yan kasa, su taimakawa gwamnati a kokarin da take yi na ganin wannan hasashe ya tabbata ta hanyar mutunta dokoki da nuna kisan kasa. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China