in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu daga cikin abubuwa da suka faru a shekara ta 2013(I)
2014-01-29 18:56:40 cri

A kowa ce shekara, abubuwa kan faru, kama daga na ban-al'ajabi, mamaki, tausayi, bajinta, takaici, tashin hankali da dai sauransu, haka lamarin ya kasance a wannan shekara ta 2013 da ta kawo karshe a ranar Talata 31 ga watan Disamba.

Baya ga ire-iren abubuwan da muka ambata a sama da kan faru a cikin kowace shekara, a kan kuma kulla dangantaka ko kai ziyarar sada zumunci tsakanin shugabannin kasashe da nufin kara karfafa dankon zumunci ko huldar cinikayya, al'adu, tattalin arziki da dai sauransu.

Misali.a watan Maris ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kasashen Rasha, Afirkat ta kudu da Tanzania, kana a ranar 21 ga watan Satumba wasu da ake zaton 'yan ta'adda ne suka kai hari kan rukunin shagunan nan na Westgate da ke Nairobi a kasar Kenya, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka tare da jikkatar wasu, baya ga asarar dukiyoyi

Kana a ranar 8 ga watan Nuwamba ne, mahaukaciyar guguwar nan ta Haiyan ta abkawa kasar Fhillippines, inda mutane sama da dubu 6 suka mutu, yayin da wasu sama da dubu 27 suka bace, kuma kasar Sin da sauran kasashe suka tallafawa kasar da kayayyakin agaji.

A shekarar ta 2013 ne kuma, tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu, mai fafutukar yaki da nuna wariyar kaunin fata, Nelson Mandela ya mutu.

Bugu da kari a wannan shekara ce kasar Sin ta harba kumbon Chang'e mai lamba 3 zuwa duniyar wata, abin da ya sanya kasar ta Sin ta zama kasa ta uku, baya ga kasashen Amurka da Rasha da suka harba kumbunansu zuwa duniyar wata da dai sauran abubuwa da suka faru a shekara ta 2013.

Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekarar 2014,Amin.(Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China