in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta himmatu wajen aiwatar da kwaskwarima a kokarin neman bunkasuwa tare da kasashen duniya
2013-12-30 15:48:50 cri

A shekarar 2013, kasar Sin ta fara aiwatar da kwaskwarima a dukkan fannoni tun bayan da sabuwar gwamnati ta haye karagar mulkin kasar.

A lokacin da aka yi cikakken zaman taro karo na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, a watan Nuwamba, an sanar da shirin kasar na zurfafa kwaskwarima a shekaru 10 masu zuwa. Shekarar 2014 ta kasance shekarar da kasar Sin ta soma aiwatar da wannan shirin, To, wane irin tasiri ne kasar Sin za ta kawo wa duniya? Yanzu ga cikekken bayanin.

Bayan manyan tarurruka biyu da kasar Sin ta saba yi a kowace shekara,na wannan karon da aka yi a watan Maris na shekarar 2013, wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a, da na majalisar wakilan jama'ar kasar, ta tattauna salon mulkin da sabuwar gwamnatin kasar Sin za ta bi domin ta bayyana a gaban duniya, wato yadda za a karfafa tattalin arzikin kasar. Sau da yawa firaministan kasar, mista Li Keqiang a wurare daban daban ya kan jaddada cewa, kasar Sin za ta kara yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje. Li yana mai cewa,

"Manyan nasarori da kasar Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki, da bunkasuwar da ta samu wajen zaman al'umma a shekaru 30 da suka gabata, an same su ne sakamakon kara bude kofa ga kasashen waje. Saboda haka, za mu ci gaba da kokarin bude kofa."

An kaddamar da yankin cinikayya cikin 'yanci a ranar 28 ga watan Satumba a birnin Shanghai na kasar Sin, hakan ya nuna dai an soma yin kwaskwarima kan harkokin kudi a kasar. A farkon watan Nuwamba ne, aka kira cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a birnin Beijing, wanda ya jawo hankulan kasashen duniya kwarai, shugaban sashen kula da harkokin Asiya da Pacific na asusun ba da lamuni ta duniya, wato IMF, mista Annop Singh ya bayyana cewa,

"Me yasa kasashen duniya suka mai da hankali sosai kan wannan taro? Kamar yadda ake cewa, kasar Sin na neman yin kwaskwarima, amma yaya za ta gudanar da wannan shiri? Mun san nasarorin da kasar ta samu, mun kuma san rawar da take takawa wajen daidaita tattalin arzikin duniya, a halin yanzu da kasashe masu ci gaba ke ciki na kokarin farfado da tattalin arziki sannu a hankali, mun fahimci tasirin da Sin ke kawo wa bukatun duniya, har illa yau dai mun fahimci cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin za ta kara inganta bunkasuwar kasashen duniya."

Wace irin hanya ce da kasar Sin za ta bi wajen yin kwaskwarima? A yayin cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an zartas da wani kuduri game da batutuwan da suka shafi zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni.

Wani masanin kasar Faransa da ke nazari kan batun kasar Sin, mista Pierre Picquart yana mai cewa,

"Kwaskwarimar da kasar Sin ke yi ya shafi kasashe daban daban na duniya. Kasar Sin ta kasance kasa ta biyu da ta fi samun ci gaban tattalin arziki a duniya, saboda haka ba kawai tana bukatar inganta bunkasuwar kanta ta hanyar yin kwaskwarima ba, har ma ta zama abin koyi ga kasashen duniya wajen tinkarar sabbin kalubaloli cikin hanzari ta hanyar daidaita manufofi."

A nasa bangaren, wani kwararren kasar Kazakhstan a fannin nazarin batun kasar Sin, mista Ruslan Izimov ya fi mai da hankali kan tasirin da kasar Sin za ta kawo wa tattalin arzikin duniya baki daya. Ya ce,

"Kudurin da aka zartas a wannan taron, ba shakka zai kawo tasiri sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta riga ta kasance babbar kasa da ta fi samun ci gaban tatttalin arziki a duniya, hakan dai tana taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman karkon tattalin arziki a wasu yankuna."

Asusun IMF ta kiyasta cewa, idan kasar Sin ta tabbatar da samun karuwar tattalin arziki na kashi 7.5 cikin 100 a shekarar 2013, to yawan gudummowar a kan karuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 27.76 cikin dari.

Shahararren masani a fannin tattalin arziki, mista Jim O'Neil, ya kimanta cewa, kasar Sin za ta zama kasa ta farko wajen ci gaban tattalin arziki a duniya a shekarar 2027. Ya ce,

"Bayan shekaru 14, adadin tattalin arzikin kasar Sin zai wuce na kasar Amurka, hakan dai za ta kawo babban tasiri a fannoni daban daban na duniya, musamman ma a fannin tattalin arziki. Sin za ta fi Amurka daukar nauyi da taka rawa a asusun IMF da bankin duniya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China