131227-harkar-ba-da-ilmi-a-talauci-danladi
|
A birnin Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ta kabilar Hui da ke da ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, dakwai wata makarantar dake karbar, dukkan daliban da suka zo daga wuraren da ke fama da talauci a kudancin jihar, wadannan yara na samun ilmi kyau, da kudin litattafai, ban da wannan kuma, daliban da ke zama a cikin makarantar suna samun kudin alawus domin amfani da su wajen sayen kayayyakin zaman yau da kullum. Wannan babbar makaranta ina kiranta da sunan Liupanshui, kuma makasudin kafa ta shi ne domin yara da ke zama a wurare da ke kan tudu masu fama da talauci su rika samun ilmi mai inganci, ta yadda za su iya cimma burinsu a zaman rayuwa a nan gaba.
Haka kuma wannan makaranta tana daya daga cikin makarantun da kasar Sin ta bude domin ilmintar da jama'a. Ganin cewa Sin kasa ce mai yawan mutane sosai, dalilin haka ne ake samun dalibai masu yawan gaske. Gwamnatin kasar Sin tana tafiyar da aikin ba da ilmi bisa babban mataki mafi girma a duniya, alkaluma sun nuna cewa, jimlar daliban dake cikin makarantu daban daban da jami'o'I daban daban a fadin kasar Sin sun haura fiye da miliyan 200.
Ayyukan ba da ilmi na kasar Sin suna hade da gidajen reron yara, da makarantun firamare da makarantun sakantare da jami'o'I da kwalejoji. Bisa aljihun Gwamnatin kasar Sin ne Dalibai suke samun ilmi daga makarantun firamare zuwa makarantun sakantare har zuwa shekaru 9 kyauta. Wadannan dalibai basu biyan kudin karatu, amma a kowace shekara za su biya kudin litattafai da sauran kudaden da basu taka kara suka karya ba.(Danladi)