131220-bayani-kan-kabilar-Yugur-Lubabatu
|
Haka kuma tarihi ya nuna cewa, yawancin 'yan kabilar Yugur suna da sunaye iri daban daban a lokacin kamar Huangfan, da Xifan da sauransu.
A shekarar 1953, bayan tattaunawa kan kananan kabilu ne aka tsai da sunan da karamar kabila ta Yugur dake ma'anar arziki da zaman lafiya.
Kiwon dabbobi ita ce babbar sana'ar 'yan kabilar Yugur, koda yake wasunsu sun juya zuwa ga aikin noma. Yankin ya kasance wurin noma da masana'antun dake sarrafa albarkatun kiwo. Haka kuma ana samun ma'adinan kwale, kana al'adar shan sayi da madara ta kasance muhimman abu ga zaman rayuwar yau da kullum ta mutanen wurin.
Bisa ga bayanan tarihi, kabilar Yugur na magana da yare guda uku, 'yan kabilar Yugur dake yankunan yamma masu cin gashin kansu na amfani da yaren Raohul; Sannan akwai yaren Engle da yawancin mutanen yankin gabashi ke amfani da shi, sai kuma harshen sinanci da 'yan kabilar Yugur dake yankin Huangnibao suke magana da shi.
Harsunan 'yan kabilar basu da bakaken kansu, bakaken harshen sinanci ne suke amfani dasu wajen rubutu a wadannan yankuna.
A shirin mu na wannan mako, za mu je da ku gundumar Sunan da ke lardin Gansu, don mu samu fahimtar yadda ake kare al'adun gargajiya na kabilar Yugur.(Lubabatu)