131213-karamar-kabilar-Yugu-ta-kasar-Sin-Danladi
|
Jama'ar Yugu tana amfani da harsuna guda biyu, wato harshen yamma, da harshen gabas, kuma abun mamaki wadanan harsuna biyu ba su da kalmomi. Dalilin haka ne bisa matakin kare harsunan kabilar Yugu, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin, da kwamitin da ke kula da harkokin kabilu na kasar Sin suka kuduri anniyar maida harsunan Yugu bisa wani matakin ayyuka na kare sunayen harsunan kananan kabilu da aka amafani dasu a duk kasar Sin, hukumomin da abin ya shafa sun gudanar da ayyuka masu yawan gaske don kare harsunan Yugu.
'Yan kabilar Yugu suna ba da gaskiya ga rukunin Gelug na addinin Buddah na Tibet, kasar Sin tana kare ayyukan addinin da 'yan kabilar Yugu suke bi, a gundumar Sunan da 'yan kabilar Yugu suke zama, ana iya samun gidanjen ibada da wuraren karatun litattafan addini, lamarin dake bayyana 'yancin 'yan kabilar Yugu na gudanar da addininsu yadda ya kamata.(Danladi)