131225-Ranar-hadin-gwiwa-tsakanin-kasashe-masu-tasowa-Sanusi
|
Bayanai na nuna cewa a shekara ta 1978 ne majalisar dinkin duniya ta bullo da wannan manufa ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da nufin bunkasa harkokin cinikayya da hadin gwiwa tsakanin hukumominsu. Ko da yake, sai a karshen shekarun 1990 ne manufar ta fara tasiri a bangaren bunkasuwa.
Ya zuwa yanzu, gamayyar ta yi taruka ne guda biyu, kuma taro na farko an yi shi ne a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a shekarar 2006, inda wakilai 53 daga nahiyar kana wakilai 12 daga kudancin Amurka suka halarci taron.
Sai dai a taron gamayyar karo na biyu da aka yi a tsibirin Margarita na kasar Venezula a watan Satumban shekarar 2009, shugabanni 49 daga kasashen Afirka ne suka halarci taron, yayin da shugabannin kasashe 12 daga kasashen kudancin Amurka suka halarci taron.
Manufar hadin gwiwar, ita ce inganta tattalin arziki, zuba jari a bangaren makamashi, mai da kafa tsarin banki na bai daya da sauransu tsakanin kasashe masu tasowa da ke cikin wannan gamayya.
Amma masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar kwalliya ta biya kudin sabulu, wajibi ne kasashe mambobin wannan gamayya, su martaba dukkan tsare-tsare da dokokin da aka cimma kana kasashe mambobi su ci moriyar juna daga dukkan fannoni. (Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)