131218-Ranar-yaki-da-cin-zarafin-mata-Sanusi
|
Ranar 25 ga watan Nuwambar ko wace shekara, rana ce da MDD ta kebe musamman domin yaki da mummunar halayyar cin zarafin mata a dukkanin fadin duniya.
Kebe wannan rana ya biyo bayan tattaunawa ta 17 da kwamiti na 3 na majalissar ya yi, yayin babban taron majalissar na 54, a ranar 19 ga watan Octoba na shekarar 1999. Yayin wannan taro ne wakilan wasu kasashe suka gabatar da wani kundin bayanai dake kunshe da kudurin kebe wannan rana.
Bayan tattaunawa kan wannan batu a ranar 3 ga watan Nuwambar wannan shekara ne kuma aka amince da hakan ba tare ma da kada kuri'u ba. Sakamakon amincewa da hakan ne kuma ya sanya babban taron MDD ke gudanar da wannan taro na baiwa mata kariya daga cin zarafin da suke fuskanta a dukkan sassan rayuwarsu.
Cikin muhimman bukatun da majalisar dinkin duniya ke fatan cimmawa karkashin wannan kuduri akwai haramta miyagun halayen da suka shafi muzgunawa mata da dakile damarsu ta cimma buri kan rayuwa, ciki har da 'yancin samun kariyar shari'a, tattalin arziki da daidaito a harkokin zamantakewar al'umma.
MDD ta fayyace dukkan wasu mataki da ka iya haifarwa mata illa ta zahiri a tunanin su a fili ko a boye a matsayin laifi da wancan kuduri ya haramta aikawata.
Yanzu haka kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi masu yawa na ci gaba da hadin gwiwa domin kare kakkokin mata a sassan duniya daban daban, duk da kalubalen dake tattare da hakan. (Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)