131129-matan-sin-na-taka-muhimmiyar-rawa-danladi.m4a
|
Matan Sin sun kara taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban a zaman al'ummar Sin. A yau za mu tattaunawa kan mata a kasar Sin.
gwamnatin kasar Sin ta ba da tabbaci ga samun ci gaban mata a fannin siyasa da kuma na dokoki. Tun tsakiyar shekarun 1990, bi da bi ne, gwamnatin kasar Sin ta tsara tsare-tsaren ka'idoji biyu kan bunkasuwar matan Sin, daya na shekaru 5, sauran kuma na 10, wadanda suka tabbatar da halalen ikon matan Sin da kuma kyautata halin da suke ciki, haka kuma sun ciyar da matan Sin gaba a fannoni daban daban.
Bisa kokarin da gwamnatin Sin da bangarori daban daban suke yi, an daukaka matsayin matan Sin sosai, kuma an kyautata halayensu a dukan fannoni, matan Sin sun riga sun shiga wani kyakkyawan mataki na bunkasuwa. A harkokin siyasa, bisa tsarin mulkin kasar Sin, matan Sin suna da iko daidai wa daida da na maza a fannin siyasa: mata suna da 'yancin zabe ko a zabe su daidai da na maza, haka kuma suna da 'yanci daidai da na maza a wajen tafiyar da harkokin kasa ko zama jami'an gwamnati. A gun taron wakilan jama'ar kasar Sin na karo na 10, yawan wakilai mata ya kai 604, wanda ya dau kashi 20.2% na dukan yawan wakilai. Kuma daga cikinsu, 21 wakilai ne na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadandan suka kai 13.2% na yawan wakilan majalisar nan. A cikin kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na zama na 10, yawan wakilai mata na kwamitin nan ya kai 373, wanda ya dau kashi 16.7% na yawan dukan wakilan wannan kwamiti.
Harkokin jin dadin al'umma da suka shirya, ciki har da shirin ba da ilmi ga yara mata da shirin zaman lafiya da ranar ba da taimako ga yaran Sin, sun sami goyon baya sosai daga gida da kuma waje, har ma an tattara kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 300, wadanda suka ba da babban taimako wajen kyautata halin rayuwar yara da ke shiyyoyi masu talauci.
A kauyuka ma, sun yi wa manoma jagoranci wajen yin watsi da miyagun al'adu da karfafa ra'ayoyin kiwon lafiya da kyautata muhalli.
Matan Afirka ma suna ta kara taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban na Afirka, har da na duniya baki daya. Akwai kuma shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson-Sirleaf, wadda ita ce zababbiyar mace shugaba ta farko a tarihin nahiyar Afirka. Wadannan fitattun mata suna kokarin neman cigaban Afirka, kuma bisa karfinsu ne suka kawo wa Afirka albarka. Bisa ga kwanciyar hankalin siyasa da saurin bunkasuwar tattalin arziki a Afirka, za a sami karin mata da ke taka muhimmiyar rawa a fagen Afirka, har ma da na duniya.(Danladi)