131211-Tasirin-wasan-kwaikwayo-wajen-isar-da-sako-Sanusi
|
Wasan kwaikwayo, wata hanya ce ta isar da sako ga al'umma, kuma saboda muhimmancin wannan kafa ko tsari, ya sa kasar Sin ta yi amfani da wasan kwaikwayo wajen nuna al'adunta ga wasu sassan duniya ciki har da nahiyar Afirka, ta yadda za su kara fahimtar zaman rayuwa da tsarin al'adun Sinawa cikin sauki tare da kara dankon zumunci tsakanin kasar Sin da al'ummomin wadannan kasashe.
Kasar Sin ta zabo wasu wasannin kwaikwayo da take ganin za su dace da zaman rayuwar kasashen Afirka, inda aka fassara su daga harshen Sinanci zuwa wasu harsunan Afirka kamar harshen Hausa da Swahili da Turanci da Faransanci da sauransu. Yanzu haka ana nuna daya daga cikin wasan kwaikwayon mai suna "Soyayyar Matasan Beijing" a gidan talabijin na NTA –Hausa Star Times a tarayyar Najeriya.
Masu fashin baki na ganin cewa, wannan wata muhimmiyar hanya ce da al'ummar Afirka za su kara fahimtar al'adu da zaman rayuwar Sinawa, kana wani bangare na bunkasa dangantakar hadin gwiwar al'adun da ke tsakamnin kasashen Sin da Afirka. (Ibrahim/Sanusi Chen)