in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin zurfafa kwakswarima da Sin ta gabatar zai yi tasiri sosai a dukkan fannoni, in ji masanin kasar Zimbabwe
2013-11-15 16:48:11 cri

Kwanakin baya an rufe cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na sha takwas, yayin taron Sin ta bayar da sakon zurfafa aikin kwaskwarima, abin da ya jawo hankalin masana na Afirka sosai.

Babbar sakatariyar cibiyar nazari da adana muhimman bayanai ta kudancin Afrika a kasar Zimbabwe Madam Johnson ta zanta da wakilin Gidan rediyon kasar Sin CRI a jiya Alhamis 14 ga wata, inda ta nuna cewa, tsarin da Sin ta shimfida a fannin zurfafa kwaskwarima ya yi hangen nesa sosai, wanda ya ba da misali mai kyau ga kasashen Afrika. Madam Johnson ta mai da hankali sosai kan bunkasuwar da Sin ta samu cikin shekaru da dama. A ganinta, cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na sha takwas ya bayyana matsayin da Sin take dauka na sa kaimi ga yin kwaskwarima, abin da ya bayyana tsarin da gwamnatin kasar Sin ke dauka wajen raya kasa a cikin shekaru goma masu zuwa. Ta ce

"Sanawar da aka bayar a gun taron ta mika wani sako ne daga gwamnatin kasar Sin na ci gaba da yin kwaskwarima,wanda ba ma kawai za a zurfafa kwaskwarima ba, har ma an tsai da shirin raya siyasa, al'umma da tsaron kasar. Sin ta zayyana hanyar da za ta bi nan gaba, taswirar yin kwaskwarima ta kasance wani tsari na dogon lokaci, wannan ya danganta da samun bunkasuwa a mataki-mataki. Duk wanda ya mai da hankali kan makomar kasar Sin, to amsar a bayyana ta ke, wato Sin tana tsayawa tsayin daka kan niyyar yin kwaskwarima."

Ban da haka, Madam Johnson ta furta cewa, tun bayan da sabbin shugabannin kasar Sin suka kama aiki, Sin ta dauki matakan da suka dace wajen kyautata dangantakar dake tsakanin saurin bunkasuwar tattalin arziki da tsarin inganta tattalin arziki, kuma ta kara bayar da muhimmanci kan samun bunkasuwar tattalin arzikin zaman al'umma cikin daidaito, a ganinta wannan hanya ce mai kyau da Sin ta zaba. Ta ce

"Yanzu sabbin shugabannin kasar Sin sun shafe tsawon shekara daya suna jan ragamar mulkin kasar. Mun lura da cewa, sun rage saurin bunkasuwar tattalin arziki domin tabbatar da dorewar bunkasuwar tattalin arzikin cikin daidaito, wannan yana da muhimmanci. Alal misali, Sin ta jaddada samun daidaito tsakanin birane da kauyuka, samar da daidaito tsakanin kamfanonin da ke karkashin kulawar gwamnati da kamfanonin masu zaman kansu."

Haka zalika, Madam Johnson ta bayyana cewa, manufofin raya kasa da kasar Sin ta dauka sun jawo hankalin kasa da kasa. Fasaha da dabarun da Sin take bi wajen tsai da manufofi na da ma'ana sosai ga kasashen Afrika. Ta ce.

"Basira da ilmi da Sin take samarwa sun baiwa kasashen Afrika damar koyon abubuwa masu kyau.Kuma kasar Zimbabwe na shirin aiwatar da tsarin sauyin hanyar da za ta bi wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin al'umma a cikin dogon lokaci, ta yadda za a samun bunkasuwa mai dorewa. A kasar Sin, hukumomin ba da shawara sun hada kai sosai da gwamnati,wannan abu ne mai kyau da ya kamata kasashen Afrika su yi koyi da shi.". (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China