in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tasirin masana'antu a nahiyar Afirka
2013-11-28 16:14:17 cri

Wannan wata muhimmniyar rana ce da gwamnatoci da sauran kungiyoyi da ke nahiyar Afirka suka kebe da nufin yin nazari game da tasirin masana'antu a nahiyar Afirka, inda ake janyo hankalin kafofin watsa labarai na kasashen duniya game da matsaloli da kalubalen da bangaren masana'antun na nahiyar ta Afirka ke fuskanta.

Bayanai na nuna cewa, babban taron shugabannin kasashe da gwamnatoci karo na 25 na kungiyar hada kan kasashen Afirka na wancan lokaci(OAU) yayin zaman da ya gudanar a kasar Habasha a watan Yulin shekarar 1989 ne, ya ayyana ranar 20 ga watan Nuwamba a matsayin ranar nazarin tasirin masana'antu a nahiyar Afirka.

Kana a ranar 22 ga watan Disamban shekarar 1989, sai babban taron majalisar dinkin duniya, ya tabbatar da wannan rana, koda ya ke an fara bikin wannan rana ce a hukumance a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1990.

Sai dai, manyan tambayoyin da ke fitowa daga bukunan masana, shi ne, ina ma'anar wannan rana, muhimmancinta a fannonin tattalin arziki, matasa, samar da abinci, sannan ko nahiyar ta shirya wajen cin gajiyar sashen masana'antun nata?

Alkaluman majalisar dinkin duniya na nuna cewa, kashi 15 cikin 100 na fadin filin duniya yana nahiyar Afirka, sannan an yi kiyasin cewa, kashi 86 cikin 100 na wannan fili ba a yi amfani da shi yadda ya kamata.

Don haka muddin, nahiyar ta Afirka tana fatan al'ummominta za su ci gajiyar wannan sashe mai tarin fa'ida, wajibi ne a inganta manufofin da za su taimakawa masana'antun kasashen na Afirka zama da gindinsu, kamar samar da makamashi, rancen kudi, fasahohi, damar yin gogayya da kamfanonin ketere da makamantansu. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China