131113-Taron-cikakken-zama-na-3na-JKS-Sanusi
|
Daga ranar Asabar 9 zuwa Talata 12 ga watan Nuwamban wannan shekarar ce, aka gudanar da cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a nan birnin Beijing, inda shugabannin suka yi nazarin hanyoyin zurfafa ayyukan yin kwaskarima daga dukkan fannoni.
Shugabannin na kasar Sin, sun bayyana cewa, gyare-gyaren da aka yi, sun shafi fannoni daban-daban kuma babu shakka za su iya ciyar da harkokin raya tattalin arzikin kasar gaba.
Masana na bayyana cewa, kwaskwarimar da kasar Sin din ta gudanar na da muhimmiyar ma'ana ga ci gaban kasar daga dukkan fannoni.
Bayan kammala taron, an gabatar da rahoton cikakken zama na wannan taro, inda al'ummar kasar da duniya baki daya, ke fatan ganin an aiwatar da jerin shawarwarin da aka cimma cikin nasara. Kuma kadan daga cikin gyare-gyaren da aka aiwatar sun hada da, barin kasuwanni su ci gashin kansu, kafa wani sabon kwamitin da zai lura da tsaron cikin gida, baiwa manoma karin ikon a kan gonakinsu.
Sauran sun hada da dokokin da suka shafi haraji da tsarin sarrafa kudaden da aka tara, jagoracin kasa bisa doka, goyon bayan bude kofa ga kasashen waje da tafiyar da harkokin mulki ta yadda zai dace da zamani, sannan uwa uba mutunta ka'idodin jam'iyya da tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin da sauransu. (Ibrahim/Sanusi Chen)