in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 ya daga huldar dake tsakanin kasar Sin da kasa da kasa zuwa wani sabon matsayi
2013-11-13 16:38:07 cri

A jiya Talata 12 ga wata ne, aka kammala cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, wanda ya jawo hankulan jama'a a gida da kasashen waje da ba a taba ganin irinsa ba. Dalili shi ne, taron zai kawo babban tasiri ga ci gaban ayyukan yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, wanda zai daga huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen duniya zuwa wani sabon matsayi.

To, masu sauraro, yanzu ga cikakken bayani da abokiyar aikinmu Bilkisu ta hada mana.

A fannin neman ci gaban kasar Sin, taron ya yi nazari kana ya zartas da kudurin kwamitin tsakiya na JKS game da muhimman batutuwan da suka shafi zurfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida a dukkan fannoni, inda za a tabo wasu muhimman matsalolin dake kawo cikas ga fannonin da suka shafi siyasa, tattalin arziki, zaman al'umma, al'adu, yanayin halittu, rundunar soja, raya harkokin jam'iyya da dai sauransu, ta yadda za a samu ci gaba, da kuma yin kwaskwarima kansu. Ana fatan samun nasara ya zuwa shekarar 2020, wajen yin kwaskwarima kan wasu muhimman fannoni da batutuwa, tare kuma da kafa wani cikakken tsarin da ya dace, da nagartattun tsare-tsare a fannoni daban daban, tare da tabbatar da su. Haka zalika tsarin gurguzu dake da halin musamman na kasar Sin zai kara samun ci gaba da kyautattuwa, za a kara zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin mulki, bunkasuwar kasar za ta kai wani sabon matsayi na karfafa inganci da cikakken karfi a dukkan fannoni, za a kara bayyana yanayi na zamani, dimokuradiyya, bude kofa ga kasashen waje, hakuri da kuma ci gaba.

A mahangar kasa da kasa, matsayin kasar Sin a harkokin kasa da kasa da kuma karfinta na fada-a-ji a duniya za su karu sosai, ban da wannan kuma, kasar za ta kara taka muhimmiyar rawa kan harkokin duniya da ayyukan yin kwaskwarima kan tsarin kasa da kasa.

Farfadowar tattalin arzikin duniya da ci gabansa zai samu moriya ne sakamakon damar da kasar Sin ta samar ta hanyar zurfafa yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni, musamman ma ta fuskar canza hanyar bunkasuwar tattalin arziki. Bisa yanayin da duniya ke ciki ta fuskantar matsalar hada-hadar kudi, matakan da kasar Sin ta dauka wadanda suka shafi habaka harkokin shigi da fice, zuba jari ga kasashen ketare, bai wa kasashen ketare tallafi, saurin karuwar masu yawon shatakawa zuwa kasashen ketare, da sauransu, dukkansu za su yi tasiri ga kasashen duniya

Bugu da kari, muhimman batutuwan dake jawo hankulan kasa da kasa da matsalolin da duniya ke fuskanta na bukatar matakan da za a iya warware su bisa matsayin da kasar Sin ke dauka, da kokarin da take yi bisa tsarin dimlomasiyya, ciki har da matsalolin nukiliyar zirin Korea, nukiliyar Iran, rikicin Syria, rikici a tsakanin Falesdinu da Isra'ila, batutuwan da suka shafi yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na duniya, magance matsalar sauyin yanayi, aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, samar da tsaro ga jiragen ruwan da ke safara a tekun Aden, rigakafi da warkar da cututtuka masu yaduwa, dukkansu ana zura ido ne kan yadda za a iya warware su sakamakon goyon da kasar Sin ke bayar wa a bangaren albarkatu gwargwadon karfinta.

Bayan haka kuma, manyan kasashen yamma, ciki har da Amurka da kasashen Turai za su kara inganta hadin gwiwa tare da Sin ta hanyar yin takara. Sa'an nan kuma, kasashen Rasha, India, Brazil, da Afrika ta kudu da wasu sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, za su zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu da Sin, wato dangantakar bangarori biyu da kuma bangarori da dama. A nasu bangaren ma, yankunan dake jawo zuba jari, da hadin kai a fannonin hada-hadar kudi, sana'o'i, da yin cudanyar al'adu da zaman al'umma, kasashen dake makwabtaka da Sin za su kai ga raya makomar al'umma, ban da wannan kuma magance matsalar bambance-bambance da rikici yadda ya kamata za ta zama burin kasashen yankin. Game da kasashen Afrika, Latin Amurka, kasashen Larabawa, za su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da Sin a fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya, da al'adu, ana sa ran irin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashe masu tasowa za ta inganta zuwa wani sabon matsayi. Sa'an nan kuma, yawan Sinawan dake aiki a kungiyoyin duniya zai kara karuwa, kasar Sin ma za ta kara samun ikon fada-a-ji a dangantakar ta bangarori da dama.

A takaice dai, a kokarin da ake na raya kasar Sin, abubuwa za su kunno kai, haka ma wasu abubuwa za su kunno kai a yunkurin da ake na bunkasa duniya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China