in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Amurka na sa ran ganin Sin ta kara bude kofa da yin kwaskwarima
2013-11-07 16:27:17 cri

A nan gaba kadan za a kira cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwamins ta Sin, a cewar masu fashin baki a Amurka dake mai da hankali kan harkokin kasar Sin, shugabannin kasar Sin za su gabatar da matakan da za su dauka yayin taron domin gudanar da kwaskwarimar da za ta kawo amfani sosai ga sauyin hanyar da Sin take yi a fannin tattalin arziki da al'umma.

Masu fashin baki a kasar Amurka sun mai da hankali kan taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da za a yi, a yayin wani taron kungiyar kwararru ta Brookings a 'yan kwanakin nan da suka gabata, darektan cibiyar mai kula da harkokin kasar Sin Jonathan Pollack ya bayyana cewa, cikakken zama na uku na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin na 18 zai jawo hankalin kasa da kasa. Ya ce

"Muna ganin yadda aka kafa yankin ciniki cikin 'yanci a birnin Shanghai, abin da ya bayyana kara bude kofa a cikin kasuwannin kasar Sin da babban yankin kasar ke yi. A sa'i daya kuma, mu'ammala tsakaninmu da shugabannin kasar Sin cikin hadda shawarwari a tsakaninsu da bangaren Amurka ya nuna alama cewa, Sin za ta fitar da karin manufar shigo da jarin kasashen waje."

Masanin tattalin arziki Mr David Dollar kana tsohon shugaban reshen kasar Sin na Bankin duniya, kuma wakilin musamman na Amurka mai kula da harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi na kasar Sin ya nuna cewa, ya kamata Sin ta zurfafa kwaskwarima da take yi a fannin saye da sayarwa, ta yadda za ta kaucewa hanyar samun ci gaba ta kashe kudi da makamashi da yawa, ban da haka, a ganinsa, yin kwaskwarima kan manufar shaidar iznin zama ta dindindin da kuma baiwa manoma damar cin riba daga manufar raya garuruwa wadanda suka kasance muhimman matakai biyu ga manufar sauya hanyar samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar. David ya ce,

"Saboda kararar mutane zuwa manyan birane, kudin shigarsu zai karu, kuma za su kara bukatunsu na sayen abubuwa. Hakan ya sa, yin kwaskwarima kan manufar shaidar iznin zama ta dinidindin na da ma'ana sosai wajen taimakawa kasar Sin tinkarar kalubalolin tattalin arziki."

Ban da haka, ya nuna cewa, kamata ya yi, a baiwa kananan hukumomin kasar Sin ikon amfani da kudi, kuma su bi hanyar da ta dace ta kara nuna haske game da harkokin kudi ta hanyar yin kwaskwarima kan harkokin hada-hadar kudi. Ya yi hasashen cewa, kwaskwarimar da za a yi za ta shafi kudin ruwa cikin 'yanci, inshorar kudin ajiye da sauransu.

Amma, babban editan jaridar labarun tsare-tsaren duniya, William Jones ya yi gargadi cewa, ya kamata, Sin ta mai da hankali kan kasuwar hada-hadar kudi yayin take aiwatar da tsarin bude kofa da yin kwaskwarima. Ya ce,

"Idan Sin ta bude kofa sosai, za a samu karin kudi sosai fiye da yadda ake tsammani cikin kasuwar kasar Sin, abin da zai haddasa hauhawar farashin kayayyaki, har ma gwamnatin kasar za ta kasa wajen daidaita wadannan matsaloli, abin da zai kawo illa sosai ga kasuwanni. A ganina, ya kamata a yi kwaskwarima, tare da yin taka tsantsan."

A ganin wasu masana, cikakken zama da za a kira ba da dadewa ba zai tabbatar da sabon buri da akala dangane da manufar bude kofa da yin kwaskwarima, wanda zai zama wata sabuwar alama dake shaida ci gaban wannan manufa a tarihi. Ko za a ci gaba da samun bunkasuwa a wannan fanni ko a'a, hakan ba kawai na da nasaba da abubuwan da za a sanar a yayin taron ba, har ma na alaka da matakan da za a dauka nan gaba da kuma nasarorin da za a samu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China