131106-matsalar-fyade-da-ake-fuskanta-a-duniya-Sanusi.m4a
|
Fyade wata babbar matsala ce da ta kasance ruwan dare gama duniya, matsalar da masana ke ganin cewa, rashin tarbiya, talauci, kallon fina finan batsa, tasirin yanar gizo, shan miyagun kwayoyi da sauransu ne ke haddasa ta.
Saboda illar wannan matsala, shi ya sa gwamnatocin kasashen da ake samun irin wannan matsala suka bullo da wasu hukunce-hukuce, wadanda suka hada da dauri na tsawo wasu shekaru a gidan yari ko hukuncin kisa, amma har yanzu babu abin da ya canza kan wannan batu na fyade.
Masu fashin baki na ganin cewa, kamata ya yi hukumomi da kungiyoyin da ke rajin kare hakkin bil-adam, su kara daukar matakan da suka dace na ilimantar da al'umma game da illar wannan matsala ga 'ya mace da kuma al'umma baki daya.
Bugu da kari, akwai bukatar mahukunta su kara tsaurara hukunci kan masu aikata wannan danyen aiki, ta yadda zai kasance darasi ga masu niyyar aikata wannan mummunan aiki da ke lalata rayuwar 'ya mace baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)