131030-an-yi-bikin-aladun-Najeriya-a-Nanjing-na-kasar-Sin-Sanusi.m4a
|
A ranar Talata 15 ga watan Oktoban wannan shekara ce, aka yi shagulgulan makon al'adun Najeriya da ma'aikatar harkokin al'adu da yawon shakatawa ta kasar Najeriya ta dauki nauyin shiryawa a birnin Nanjing da ke nan Kasar Sin.inda aka yi nune-nunen al'adu, kayayyakin gargajiya, harkokin yawon shakatawa da fasahohin kasar Najeriya da sauransu ga mazauna birnin Nanjing.
Ministan harkokin al'adu da yawon shakatawa na kasar Najeriya Edem Duke ne ya jagoranci tawagar ta Najeriya a wannan biki, yayin da mataimakin darekta a sashen lura da cudanyar kasashe na kasar Sin Zhao Haisheng ya kasance jami'in bangaren Sin a bikin.
Najeriya dai ta kasance kasa ta farko dake nahiyar Afirka da ta kafa cibiyar al'adunta a kasar Sin. Kuma ta kaddamar da aikin yada al'adun Najeriya wanda aka kwashe mako guda cur ana yinsa a kowace shekara. Kasar Sin kuma ta goyi bayan ayyukan da Najeriya ta yi a wannan fanni, hakan ya sanya aikin yin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu a wani sabbin matsayi a tarihi, ganin yadda a karo na farko Sin ta fara shiga shagalin nuna al'adun Najeriya a Abuja a shekarar bara, sannan a karo na farko da birnin Nanjing na kasar Sin ya kulla dangantakar hadin kai a fannin al'adu da Najeriya, sannan a karo na farko da Sin ta shiga bikin baje kolin kayayyakin fasaha na Afirka da ya gudana a Najeriya a wannan shekara da muke ciki, hakazalika a karo na farko da Najeriya ta kaddamar da bikin nuna al'adunta a kasar Sin a shekarar bara.
Masana na ganin cewa, wannan biki wani babi ne mai zaman kansa cikin gundarin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, matakin da masu fashin bakin ke cewa,yana taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar kasashen biyu daga dukkan fannoni. (Ibrahim/Sanusi Chen)