131023-kasashen-duniya-na-fuskantar-matsalar-karancin-abinci-Sanusi.m4a
|
Ana bikin wannan rana ce ranar 16 ga watan Oktoban kowa ce shekara,don karrama ranar da aka kafa kungiyar samar da abinci da aikin gona ta MDD(FAO) da aka yi a shekarar 1945.
Bayanai na nuwa cewa,kasashe mambobin shirin na FAO ne suka kafa wannan rana a babban taron kungiyar karo a 20 a watan Nuwamba na shekarar 1945.
Tun wannan lokaci,a kowa ce shekara, akan bullo da taken bikin da zai kasance, kamar yakar yunwa don rage talauci,zuba jari a bangaren aikin gona don kara samar da abinci da dai sauransu.
Sai dai duk da kokarin da gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa ke yi na samar da abinci,har yanzu ana fuskantar matsalar abinci a duniya,inda yunwa da tamowa suka kasance manyan matsalolin da dan-adam ke fama da su har zuwa wannan lokaci.
Bisa rahoton da shirin samar da abinci na duniya(WFP) ya nuna,yanzu haka akwai mutane kimanin miliyan 870 a duniya da ke fama da matsalar yunwa,koda ya ke matsalar ta ragu idan aka kwatanta da shekarar 2009.
Amma alkaluma na nuna cewa, akwai babban gibi sosai tsakanin burin rage rabin yawan mutanen da ke fama da yunwa a shekarar 2015 da majalisar dinkin duniya ta gabatar. Sassan rahoton na WFP ya ce, saboda karuwar yawan jama'a a duniya,yawan bukatar abinci a duniya a shekarar 2050 za ta karu da kashi 60 cikin 100 bisa na yanzu.
Sannan masana na bayyana cewa, bala'u da raguwar filayen noma ko gonaki, za su yi tasiri ga farashin kayan abinci a duniya,wadannan da sauran matsaloli suna daga cikin abubuwa da masana ke ganin ya kamata a kara daura damarar magance su, muddin ana son a kawar da matsalar abinci da jama'a ke fama da ita a duniya.(Ibrahim/Sanusi Chen)