131018-babbar-sallah-a-kasar-Sin-lubabatu
|
Kasar Sin kasa ce da ke da dimbin musulmi, wadanda yawansu ya kai sama da miliyan 20. A nan kasar, akwai kabilu 10 da suke bin musulunci, cikinsu akwai kabilar Hui, Uygur, Kazak, Uzbek da sauransu, wadanda akasarinsu ke da zama a jihohin Xinjiang, Gansu, Ningxia, Qinghai da dai sauran sassan arewa maso yammacin kasar. A ranar 15 ga watan Oktoba ne, al'ummar musulmin kasar Sin suka fara bukukuwan murnar babbar sallah ta wannan shekara.